in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta kudu da kamfanin Sin za su fara gina hanyoyin mota a kasar
2019-03-27 10:32:20 cri

Kasar Sudan ta kudu ta daddale wata yarjejeniya da kamfanin kasar Sin wato rukunin Shandong Hi-Speed domin gudanar da aikin gina wasu manyan hanyoyin mota a kasar wadanda za su hade yankunan karkara na kasar da babban birnin kasar Juba.

Rebecca Joshua Okwaci, ministar kula da hanyoyin mota da gadoji ta kasar ta bayyana cewa, aikin zai taimaka wajen kyautata zaman lafiya, baya ga taimaka wajen bunkasa ciniki, aikin zai kuma taimaka wajen sada zumuntar al'ummar kasar bayan shafe shekaru biyar ana fama da tashin hankali a kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China