in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin Sin ya horar da injiniyoyi 20 'yan kasar Sudan ta Kudu kyauta
2018-06-18 15:36:40 cri

Kamfanin shimfida layin dogo na kasar Sin ya ba da horo kyauta ga injiniyoyi 20 matasa 'yan kasar Sudan ta Kudu.

A baya-bayan nan ne, matasan da suka karanci fannonin aikin injiniya daban-daban da suka hada da na gine-gine da na lantarki da kafinta, suka kammala karbar horo na tsawon wata guda, karkashin wani shirin tallafi na kasar Sin da ke da nufin zamanantarwa da fadada babban asibitin koyarwa na Sudan ta Kudu dake birnin Juba.

A cewar kamfanin na kasar Sin, dalibai 20 ne suka nemi gurbin karbar horon, kuma daga cikinsu 7 ne kadai suka kammala, wadanda kuma za su samu damar aiki da shi.

Deng Agany Aguto, wanda ya kammala karatun injiniya daga jami'ar kasar Rwanda, ya ce ya koyi da'a da jajircewa da sanin ya kamata, wadanda sune muhimman abubuwa a aikin injiniya.

Ya kara da cewa, ya ji dadin aiki da Sinawa, saboda a kasarsu, babu kayayyaki na zamani, inda ya bayyana horon da ya samu a matsayin mai muhimmanci.

A nasa bangaren, Benjamin Bol, wanda ya karanci aikin injiniya na fannin gine-gine a jami'ar birnin Juba, ya bayyana injiniyoyin Sinawa a matsayin masu basira, inda ya bayyana banbancin harshe a matsayin kalubale daya da suka fuskanta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China