in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Likitoci Sinawa sun duba lafiyar yara kyauta a Sudan ta Kudu
2018-06-02 15:44:17 cri

Ayarin likitoci Sinawa dake Sudan ta Kudu, sun duba lafiyar yara kyauta tare da ba da tallafin abinci, a wani gidan marayu mallakar gwamnati a birnin Juba, a wani bangare na bikin ranar yara ta duniya.

Kashi na 6 na likitocin kasar Sin, sun duba yara dake da matsalar idanu da ta fata, kana sun ba da gudunmuwar kayayyakin abinci domin bunkasa musu sinadaran gina jiki.

Shugaban ayarin likitocin Sun Yaxi, ya ce yara kyakkyawan fata ne ga kowace kasa, kuma akwai dimbin gudumuwar da za su iya badawa. Ya ce, ga Sinawa, idan yara na cikin koshin lafiya, to kasa ma na nan lafiya. A don haka, dole ne yara su samu kulawa daga al'umma.

A nasa bangaren, Isaac Maker, babban daraktan asibitin koyarwa na Juba, ya yabawa rawar da likitocin Sinawa ke takawa, inda ya ce, al'ummar Sudan ta kudu sun amfana sosai da likitocin kasar Sin cikin shekaru 5 da suka gabata.

Ya ce, yana matukar godiya ga ayarin likitocin, ba wai kawai don gudummuwar da suka ba marayun ba, a'a, don tashi da suka yi daga kasar Sin zuwa Sudan ta kudu, don ba da taimakon kiwon lafiya ga jama'a.

Ya kuma yaba da kaunarsu ga yaran, yana mai cewa, abun da suka yi zai sauya rayuwar yara, kuma za su rika tunawa da al'ummar Sinawa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China