in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ARC na shirin bullo da matakan kandagarkin bala'u a Afirka
2019-03-27 10:11:07 cri

Hukumar kungiyar tarayyar Afirka da ta kware wajen kare aukuwar bala'u (ARC), ta bayyana cewa, tana nan tana kokarin bullo da wasu dabaru, don taimakawa yadda kasashen nahiyar za su shirya tunkarar bala'u daga indallahi, kamar mahaukaciyar guguwa.

Darektan hukumar ta ARC Mohamed Beavogui, ya ce hukumar, tana shirin tsara ambaliyar kogi da mahaukaciyar guguwa na gwaji.

Hakan a cewar darektan, zai taimakawa kasashen nahiyar dake fuskantar barazana samun kudade, ta yadda za su taimakawa al'ummomin da irin wadannan bala'u ya shafa a kan lokaci.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China