Shugaban kasar Masar, Abdel Fattah al-Sisi, ya lashi takobin kara karfafa hadin gwiwar tsaro da kasar Sin, yayin da yake ganawa da mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan tsaron kasar, Wei Fenghe dake ziyara a Masar.
Yayin ganawar a jiya Litinin, Abdel Fattah al-Sisi, ya tunatar da dadewar dangantakar dake tsakanin Sin da Masar, inda kasashen biyu suka samu kyawawan sakamako a dukkan fannoni, yana mai bayyana irin gudunmuwar da Sin ke bayarwa ga zaman lafiya a duniya.
Ya kuma jinjinawa nasarorin da kasar Sin ta samu a ci gabanta, yana mai cewa, Masar na goyon bayan shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, kuma yana sa ran kara karfafa hadin gwiwa da kasar Sin a fannin ginin ababen more rayuwa.
Shugaba al-Sisi ya kuma bayyana fatan bangarorin biyu za su inganta hadin gwiwarsu a bangaren tsaro da kara hadin gwiwa a fannonin yaki da ta'addanci da horon kwancen soji domin karfafa aikin soji da ma bangaren tsaro.
A nasa bangaren, Wei Fenghe, ya ce kasar Sin na yabawa muhimmiyar rawar da Masar ke takawa a batutuwan da suka shafi shiyyarta da kuma kasa da kasa, kana tana goyon bayan kokarin Masar na kare cikakken iko da 'yancinta.
Jami'in na kasar Sin ya kara da cewa, a shirye kasar Sin take ta kara hada hannu da Masar domin inganta shawarar Ziri Daya da Hanya Daya da nufin kara habaka dangantakar dake tsakaninsu. (Fa'iza Mustapha)