in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masar: Kafa yankin cinikayya a sabon birnin kasar babban aikin hadin gwiwa ne da Sin
2019-01-15 10:32:05 cri

Firaministan kasar Masar Mostafa Madbouly, ya ce kafa yankin hada hadar cinikayya da kasuwanci a sabon birnin da kasar ke ginawa, daya ne daga manyan ayyukan hadin gwiwa da Masar ke gudanarwa tare da kasar Sin.

Kamfanin dillancin labarai na MENA ya rawaito firaministan na cewa, wannan aiki wani gagarumin ci gaba ne a sabon zamani da ake ciki. Jami'in na wannan tsokaci ne a jiya Litinin, lokacin da yake rangadi a harabar yankin cinikayyar na musamman dake sabon birnin, wanda kamfanin gine gine na kasar Sin CSCEC ke aiwatarwa.

Yanzu haka dai kamfanin CSCEC na aikin gina katafaren yankin na hada hadar cinikayya a sabon birnin da aka tsara a Masar, wanda ke da nisan kilomita 50 gabas da birnin Alkahira, fadar mulkin kasar.

Mr. Madbouly ya ce, aikin ya kushi manyan gine gine masu hawa 20, da hasumiyoyi da za su samar da dunbin guraben ayyukan yi, ciki hadda wata hasumiya mai tsayin mita 385, wadda za ta kasance mafi tsayi a dukkanin nahiyar Afirka.

Babban jagoran kamfanin CSCEC ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, za a kammala ginin yankin hada hadar cinikayyar da aka fara a bara, cikin shekaru uku da rabi masu zuwa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China