in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rashin ci gaban aikin gona na yin cikas ga yunkurin kawar da talauci a Tanzaniya
2018-05-03 10:01:32 cri

Ministan kudin Tanzaniya Philip Mpango ya ce, ci gaban tattalin arzikin kasar da kaso 7 bisa dari bai yi tasiri kan rayuwar al'ummar kasar da har yanzu ke fama da talauci ba.

Philip Mpango, wanda ya bayyana haka ga wani taron manema labarai, yayin taron shekara-shekara na gidauniyar bincike kan tattalin arziki da rayuwar al'umma karo na 7 da ya gudana a cibiyar tattalin arzikin kasar Dar es Salam, ya ce alakanta tabarbarewar al'amura da tafiyar hawainiya da bangaren aikin gona ke yi kan kaso 3.3 bisa dari, idan aka kwatanta da kaso 16 bisa dari da ake samu a bangaren hakar ma'adinai a kowacce shekera.

Ministan ya ce, kaso 60 na al'ummar kasar, wato kusan mutane miliyan 54 na aiki ne a bangaren aikin gona.

Philip Mpango ya ce, gwamnati ta dauki dabaru da manufofin bunkasa bangaren, sai dai, bai yi karin bayani kan su ba.

Ya kuma bayyana karuwar adadin jama'a a matsayin karin dalilin dake haifar da talauci.

Ya ce, yayin da adadin al'ummar kasar ya karu cikin sauri, albarkatunta na nan a yadda suke. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China