in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Sin: Ziyarar shugaba Xi a Monaco zata inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu
2019-03-24 16:45:17 cri
Bisa gayyatar da shugaban karamar daular Monaco yarima Albert na biyu ya yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai ziyarar aiki a karamar daular, wannan ne kuma zai kasance ziyarar ta farko da shugaban Sin zai yi a Monaco. A yayin da yake zantawa da manema labaru na CMG, jakadan kasar Sin dake Monaco Zhai Jun ya bayyana cewa, ziyarar ta shugaba Xi zata ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu gaba, tare kuma da nuna abin koyi wajen tabbatar da zaman daidai wa daida da sada zumunci a tsakanin babbar kasa da karamar kasa.

Zhai ya kara da cewa, Monaco wata kasa ce ta musamman. Akwai bambanci sosai a tsakanin kasashen Sin da Monaco. Ga misali, kamar yadda aka sani, kasar Monaco na da muraba'in kilomita 2.02 kawai, wadda ta kasance kasa mafi kankanta ta biyu a duniya. A nata bangaren, kasar Sin kasa ce mafi girma ta uku a duniya wajen fadin kasa. Amma, duk da haka, ba a hana inganta kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a cikin dogon lokaci ba. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China