in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin da Italiya sun yi shawarwari a tsakaninsu
2019-03-23 16:51:32 cri

 

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Italiya Sergio Mattarella Jiya Jumma'a, bisa agogon Rome, inda suka amince da raya huldar da ke tsakanin kasashen 2, bisa hangen nesa da kuma manyan tsare-tsare, a kokarin kara bunkasa huldar abota a tsakaninsu cikin sabon zamani.

A yayin shawarwarin, shugaba Xi Jinping, ya jaddada cewa, wajibi ne kasashen 2 su kara tuntubar juna ta fuskar tunani da inganta amincewa juna ta fuskar siyasa, da ci gaba da kyautata fahimtar juna da mara wa juna baya kan batutuwan da ke shafar babbar moriyarsu da kuma wadanda ke jan hankalinsu. Ya kara da cewa, akwai bukatar su kara kyautata mu'amala da hadin gwiwa tsakanin gwamnatoci da hukumomin kafa doka da jam'iyyu. Kana dole ne kasashen 2 su habaka fannonin yin hadin gwiwa, tare da hada kai wajen raya shawarar "ziri daya da hanya daya". Shugaba Xi Jiping ya ce kasar Sin na son kara sayen kayayyakin Italiya masu inganci, da karfafawa karin kamfanoninta gwiwar zuba jari da yin kasuwanci a Italiya. Haka zalika, kamata ya yi kasashen 2 su inganta mu'amalar al'adu, domin kara samun fahimtar juna tsakanin jama'arsu.

A nasa bangaren, Shugaba Mattarella ya ce, Italiya na goyon bayan shawarar "ziri daya da hanya daya" da shugaba Xi Jinping ya gabatar, ta kuma yi imanin cewa, shawarar za ta amfana wajen hada nahiyoyin Turai da Asiya da kuma ci gabansu tare. Ya ce shawarar za ta kara sabon kuzari kan tsohuwar hanyar siliki a wannan zamanin. Har ila yau, ya ce Italiya tana son inganta mu'amala da hadin gwiwa da kasar Sin ta fuskar al'adu da yawon shakatawa. Shugaban ya ce Italiya ta yi imanin cewa, farfadowar kasar Sin za ta ba da sabuwar gudummowa wajen wanzar da zaman lafiya da wadata a duniya. Kuma kasarsa tana himmantuwa wajen sa kaimi kan ci gaban huldar da ke tsakanin kasashen Turai da Sin. Bugu da kari, tana son kara tuntubar kasar Sin da taimakawa juna cikin ayyukan MDD da kungiyar G20 da sauran hukumomin duniya, a kokarin kiyaye kasancewar rukunoni da dama a duniya da yin ciniki cikin 'yanci, da daidaita kalubalen sauyin yanayi da tsaron kasa da kasa tare.

1  2  3  
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China