"Kamar yadda na ce, Sin da Faransa kawaye ne na musamman, kana abokan hulda na moriyar juna. Duniya na fuskantar kalubalen da ba a saba gani ba kuma dan Adam na wani muhimmin gab'a na ci gaba. Kalubale da haduran da muke tunkara na kara zama mai sarkakiya, kuma damarmakin da muke samu, ba a taba ganin irinsu ba. A matsayin muhimmiyar abokiyar huldar Faransa, kasar Sin za ta ci gaba da tafiya da Faransa kafada-da-kafada. Ina fatan bangarorin biyu za su yi amfani da damar da suka samu, su kuma hada hannu wajen tunkarar kalubale da zurfafa amincin dake tsakaninsu domin fadada kokarinsu na samun ci gaba na bai daya da kyakkyawar makoma ga kowa.
"Sinawa sun yi amana cewa, tafiyar mil dubu na farawa ne da taku na farko, yayin da Victor Hugo ya ce 'lokaci kalilan ya isa a sauya komai'. yanzu mun tsaye a mafari. Bari kasar Sin da Faransa su hada hannu su fara tafiya mai kwari zuwa ga samar da sabuwar dangantaka mai karfi da buri na bai daya tsakaninsu." (Fa'iza Mustapha)