in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadin gwiwa tsakanin Sin da Turai za ta samu "sabon karfi" sakamakon ziyarar da Xi Jinping zai kaddamar a Turai
2019-03-20 19:37:24 cri

A lokacin da yanayin duniya yake da dumi dumi a watan Maris, daga ranar 21 zuwa 26 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kaddamar da ziyararsa ta aiki a kasashen Italiya da Monaco da kuma Faransa. Shugaban kasar Sin ya zabi wasu kasashen Turai don fara ziyararsa ta farko a ketare a bana, lamarin da ya jawo hankulan duniya sosai, yayin da ake fitar da cikakkun bayanai. A yau Laraba, wani babban jami'in ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a nan Beijing cewa, wannan ziyara tana da muhimmancin gaske ga huldar dake tsakanin kasar Sin da wadannan kasashen Turai 3, kuma za ta sanya sabon karfi ga kokarin bunkasar huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Turai, har ma za a bude sabon babi ga kokarin aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya" da ake yi cikin hadin gwiwa, ta yadda kasar Sin za ta iya bayar da nata sabuwar gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a duniya baki daya.

Bana shekaru 15 ke nan da aka kulla huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen Sin da Italiya, sannan badi shekaru 50 da kulla dangantakar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu. Game da yadda za a yi hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu bisa shawarar "ziri daya da hanya daya" da yake jawo hankulan sauran kasashen duniya, a yayin wani taron manema labaru, Mr. Wang Chao, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, "Bangarorin Sin da Italiya dukkansu na mai da hankali sosai kan yadda za su yi hadin gwiwa bisa shawarar 'ziri daya da hanya daya'. Mun gamsu da yadda bangaren Italiya ya amince da shawarar. A ganinmu, takardun hadin gwiwa da muka kulla sun dace da moriyarmu. Sakamakon haka, bangaren Sin na fatan yin hadin gwiwa da bangaren Italiya wajen yin hadin gwiwar da ta dace, ta yadda za su cimma nasara tare. Kawo yanzu, yawan kasashe da yankuna da kuma kungiyoyin kasa da kasa da suka sanya hannu kan takardar yin hadin gwiwa da bangaren Sin bisa shawarar 'ziri daya da hanya daya' ya wuce 150, galibinsu sun riga sun samu moriya daga wannan shawara. Idan bangarorin Sin da Italiya za su iya cimma matsaya daya kan ayyuka masu alaka da shawarar 'ziri daya da hanya daya', ko shakka babu, zai yi kyakkyawan tasiri ga bunkasar tattalin arziki da hadin gwiwar moriyar juna ga kasashen biyu."

Kasar Monaco tana maraba da ziyarar aikin shugaban kasar Sin karo na farko da zai kai nan ba da jimawa ba. Wang Chao ya nuna cewa, a lokacin ziyararsa, shugaba Xi Jinping zai gana da sarki Albert II, a kokarin raya huldar da ke tsakanin kasashen 2 zuwa sabon zamani.

Kasar Faransa, ita ce zango na karshe a ziyarar aikin shugaba Xi Jinping a Turai. Bana, shekaru 55 ke nan da kulla huldar jakadanci a tsakanin Sin da Faransa, kana ziyarar aikinsa ta biyu da shugaba Xi Jinping zai kai Faransa bayan shekaru 5. Wang Chao ya bayyana cewa, "Muna fatan yin amfani da ziyarar aikin shugaba Xi Jinping a Faransa da kuma cika shekaru 55 da kulla huldar jakadanci a tsakanin kasashen 2, wajen hada kai da Faransa domin inganta amincewa da kuma fahimtar juna, a kokarin kara daga matsayin hadin gwiwarsu, kara samun moriyar juna, taka muhimmiyar rawa a fannonin kiyaye tunanin kasancewar bangarori daban-daban a duniya, da kyautata tafiyar da harkokin duniya yadda ya kamata, da taimakawa kasashen duniya su daidaita kalubale tare cikin himma, da kara kawo wa jama'ar kasashen 2 alheri. "

Kafofin yada labaru na kasashen waje sun lura da cewa, yayin ziyarar shugaban kasar Sin ta farko ta bana, ya zabi nahiyar Turai don ta zama wurin farko da zai yada zango, hakan a cewar kafofin yada labarun, ya nuna yadda kasar Sin take dora muhimmanci sosai kan nahiyar Turai.

A nasa bangaren, Wang Chao, mataimakin ministan harkokin wajen kasar ta Sin, ya furta a yau Laraba cewa, ziyarar shugaban kasar Sin Xi Jinping a nahiyar Turai za ta kara kokarin raya huldar dake tsakanin Sin da Turai, tare da amfanawa karin al'ummonin bangarorin 2. Wang ya ce,

"Wannan ziyarar da shugaba Xi Jinping zai kai a kasashen Turai za ta kasance wani batu mai matukar muhimmanci ga aikin hulda da nahiyar Turai da kasar Sin ke yi. Muna sa ran ganin shekarar bana ta zama wani lokaci na samun kyautatuwar huldar dake tsakanin Sin da Turai, sa'an nan hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin 2 ta samar da wani yanayi mai kyau ga duniyarmu a shekarar 2019 da muke ciki. Kasar Sin na son zurfafa musayar ra'ayi da hadin gwiwar da take yi tare da bangaren Turai, da zummar raya huldar dake tsakanin bangarorin 2, da tabbatar da dorewar ci gabanta, gami da samar da karin gudunmmawa ga kokarin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a duniya." (Sanusi, Tasallah Yuan, Bello)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China