in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Huldar dake tsakanin Sin da EU za ta shiga "Zamani Muhimmi"
2019-03-19 17:48:23 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kaddamar da ziyararsa ta aiki a kasashen Turai guda uku wato, Italiya da Monaco, da kuma Faransa a Alhamis mai zuwa, ziyarar da ta kasance ziyara ta farko da shugaban kasar Sin zai kai a ketare a shekarar da muke ciki, a don haka ana tsammanin cewa, ziyarar tana da ma'ana ta musamman, a fannonin huldar tattalin arziki da kasuwanci, da shawarar "ziri daya da hanya daya", da cudanyar al'adu da sauransu.

Hakika huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Turai tana kawo babban tasiri ga sassan biyu da bangarori daban daban, da ma duk fadin duniya baki daya. Kamar yadda ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana cewa, cikin sauki ana iya fahimtar makasudin ziyarar da shugaba Xi zai kai a kasashen Turai wato duk da cewa yanayin da kasashen duniya ke ciki ya gamu da manyan sauye-sauye, amma har kullum kasar Sin tana mayar da huldar dake tsakaninta da kasashen Turai a matsayin koli yayin da take gudanar da huldar diplomasiyya, shi ma ya yi hasashen cewa, ziyarar da shugaba Xi zai kai a kasashen za ta shiga "Zamani Muhimmi" kuma za ta bude wani sabon shafi na huldar dake tsakanin sassan biyu wato kasar Sin da kungiyar tarayyar Turai wato EU.

"Zamani Muhimmi" lokaci ne da aka bullo da abubuwa masu kyau wajen hadin kan Sin da Turai. Da farko, aka soma "Zamani Muhimmi" da dangantakar dake tsakanin Sin da Turai ne sakamakon jagorancin shugabannin bangarorin biyu. A shekaru 5 da suka gabata, a yayin da shugaba Xi ke ziyara a Turai, sai ya bayyana cewa, kamata ya yi a duba dangantakar dake tsakanin Sin da Turai bisa manyan tsare-tsare, ya kamata a hada kan Sin da Turai a fannonin karfinsu, da kasuwanninsu, da al'adunsu, don kafa dangantakar abokantaka irin ta zaman lafiya, bunkasuwa, kwaskwarima, al'adu a tsakanin Sin da Turai.

A karkashin irin manufar, Sin da Turai sun mai da hankali kan neman hadin kai irin na samun nasara tare a cikin 'yan shekarun nan, har ma suka samu sabon ci gaba a fannoni daban daban, ta yadda bangarorin biyu ke samun bunkasuwa a fannonin moriyar bai daya, matsayin bai daya, da kuma burin bai daya.

Alal misali, zangon farko a ziyarar shugaba Xi Jinping a Turai a wannan karo shi ne Italiya, kasa ce da shugaban kasar Sin ya taba ziyara yau shekaru goman da suka gabata. Kafin shugaba Xi ya tashi, ya samu wata wasika da daliban makarantar "Vittorio Emanuele II" ta Rome suka rubuta masa, inda suka ce, a shekara daya da ta gabata, sun karanta littafin "Ra'ayin Xi Jinping Kan Yadda Za'a Mulki Kasa Da Tafiyar Da Hakokinta", inda Xi ya bayyana burin da kasar Sin take son cimmawa. Daliban sun rubuta cewa, tun daga lokacin da ya zuwa yanzu, ko kasashen gabashin duniya, ko na yammacin duniya, dukkansu na da kyakkyawan fata game da zaman jin dadi. Shugaba Xi ya maido musu amsa ba tare da bata lokaci ba, inda ya baiwa daliban kwarin-gwiwar su zama tamkar mala'ika tsakanin Sin da Italiya wajen mu'amalar al'adu. Amsar wasikar da Xi ya rubuta wa daliban Italiya ta faranta musu rai sosai, al'amarin da ya sa karin matasan Italiya suka kara fahimtar babbar darajar al'adun kasashen biyu.

Sin da Turai sun soma "Zamani Muhimmi" kan dangantakarsu ne sakamakon matsayin da suke tsayawa na bunkasa kyakkyawar huldar dake tsakanin bangarorin biyu dake kasancewar bambancin tsarin kasa. Kasar Sin da wasu kasashen Turai da dama suna da bambanci sosai kan al'adun tarihi da tsarin al'umma, kana akwai bambanci a matsayinsu na ci gaba, suna kuma yin takarar kasuwa a fannonin tattalin arziki da cinikayya, amma duk da haka ba a hana ci gaban hadin kai yadda ya kamata a tsakaninsu. Sin da Turai manyan abokan cinikayyar juna ne, a watanni biyu na farkon shekarar bana, jimilar cinikayya a tsakanin bangarorin biyu ta kai RMB biliyan 737.63, wato ta karu da kashi 8.9 cikin dari, wadda ta kai kashi 16.2 cikin dari bisa na jimilar cinikayyar waje ta kasar Sin. Dalilin shi ne, ko da yaushe bangarorin biyu ke mai da neman samun nasara tare a matsayin buri da tushe na hadin kansu.

Alal misali na dangantakar dake tsakanin Sin da Faransa, tun daga kasar Faransa ta karbi dabilai daga kasar Sin karo na farko da suka zo da karatu tare da yin aiki a shekaru 100 da suka gabata, da kuma Faransa ta zama kasa ta farko ta yammacin duniya da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninta da kasar Sin a shekaru 55 da suka gabata, kasashen biyu suna kiyaye yin kokarin neman samun moriyar juna bisa bukatun samun ci gaba nasu. An ce, don horar da kwararru a fasahohin zamani, gwamnatin kasar Sin ta riga ta maida aikin horar da kwararru a matsayin daya daga cikin manyan ayyukan da za a gudanar a bana, don haka wannan fanni zai kasance muhimmin fannin da kasashen biyu suka yi hadin gwiwa da juna wajen inganta wa. Birane da yankunan sada zumunta na Sin da Faransa 200 za su fara yin hadin gwiwa wajen bada ilmin fasahohi da horar da kwararru.

Dalilin da ya sa huldar da ke tsakanin Sin da Turai ta kai wani mataki saurin karfafuwa, shi ne sabo da rashin tabbas da ake fuskanta na duniya na bukatar Sin da kasashen Turai su kara hada kan juna, da kuma amincewa da juna. Bayan shiga shekarar 2019, duniyarmu na ci gaba da fuskantar rashin tabbas, musamman ma a nahiyar Turai, inda a yayin da ake fama da ra'ayin kashin kai, da manufar kariyar ciniki da ma ta'addanci, za a kuma gudanar da zaben kungiyar tarayyar Turai. A irin wannan halin da ake ciki kuma, ana bukatar huldar da ke tsakanin manyan kasashe ta tafi yadda ya kamata, kuma ta samar da kwanciyar hankali ga duniya. Yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai ziyara kasashe uku na nahiyar Turai a farkon wannan shekara, hakan ba kawai zai tabbatar da hadewa da juna tsakanin Turai da Asiya bisa shawarar ziri daya da hanya daya ne, har ma zai kuma bude wani sabon babi na tabbatar da zumunta da juna, da kuma hadin gwiwa da juna a tsakanin kasashen shiyyar.

Yanzu haka ana yin takara tsakanin kasar Sin da kasashen Turai a wasu fannoni, amma a galibin lokuta, bangarorin 2 suna kokarin hadin kai da juna. Yayin da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi jawabi a lokacin da yake ziyara a kasashen Turai wasu shekaru 5 da suka wuce, ya ce, dalilin da ya sa aka samu wasu ra'ayoyi marasa dacewa shi ne, domin akwai wasu abubuwan da suka hana su fahimtar juna. Ya kuma tsamo maganar Gottfried Leibniz, wato shahararren masanin falsafa na kasar Jamus, da ya ce, "Musayar fasahohinmu kawai ke iya taimakawa kara basirarmu". Yanzu shekaru 5 sun shude, kuma muna fatan ganin wannan "Zamani Muhimmi" na taruwar shugabannin Sin da kasashen Turai zai zama wata damar kara basira, don samar da wani kyawawan yanayi ga duniyarmu dake fama da rashin tabbas. (Jamila, Bello, Lubabatu, Murtala, Bilkisu, Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China