#2019Taruka2# Kasar Sin zata dauki matakan bunkasa cinikin waje da zuba jari cikin 'yanci
A cikin rahoton da gwamnatin kasar Sin ta gabatarwa majalisar kolin mulkin kasar a yau Talata, gwamnatin ta bayyana cewa, za ta ci gaba da bin manufar raya harka tare, tattaunawa tare, raba moriya a yayin da take yin hadin gwiwa da sauran kasashen duniya wajen samar da makamashi da kayayyaki da kuma habaka hadin gwiwa a kasuwannin ketare. Sannan zata ciyar da shawarar "ziri daya da hanya daya" gaba, da kuma shirya taron koli karo na biyu na yin hadin gwiwa bisa shawarar "ziri daya da hanya daya". Bugu da kari, tabbas ne kasar Sin za ta yi kokarin tabbatar da bunkasa tattalin arziki a duk fadin duniya baki daya da yin cinikayya tsakanin kasa da kasa ba tare da shinge ba. Bugu da kari, za ta yi kokarin hanzarta yin gyare-gyaren da ake yi kan kungiyar cinikayya ta duniya WTO.
A kullum, kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan matsayin kawar da ringingimun cinikayya ta hanyar yin tattaunawa bisa adalci, kuma tabbas ne za ta ci gaba da cika alkawuran da ta dauka, amma tabbas ne za ta kare moriyarta bisa doka kamar yadda ya kamata. (Sanusi Chen)