Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta sanar a jiya Litinin cewa, tsohon firaiministan kasar Sao Tome da Principe, Joaquim Rafael Branco, zai jagoranci tawagar AU mai sa ido a zaben da za'a gudanar a jamhuriyar Guinea-Bissau a wannan mako.
Ana sa ran tagawar ta AU za ta sanya ido kan zaben majalisar dokokin Guinea-Bissau, wanda aka shirya gudanarwa a ranar 10 ga watan Maris.
Tawagar sa idon ta AUEOM, wadda Branco ke jagoranta, ta kunshi jami'an sa ido kimanin 30 wadanda aka tura don sanya ido a zaben majalisar dokokin kasar ta Guinea-Bissau wanda aka fara shirye shiryensa tun a ranar 2 zuwa 16 ga watan Maris, wata sanarwa daga AU ne ta tabbatar da hakan a jiya Litinin.
A cewar kungiyar ta AU, babbar manufar shirin sa idon a zaben ita ce don ba da gudunmowa wajen kyautata zaman lafiya da kwanciyar hankali a Guinea-Bissau da ma Afrika baki daya.(Ahmad Fagam)