in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya yi maraba da ci gaban siyasa a Guinea-Bissau
2018-04-20 10:42:04 cri

Kwamitin tsaron MDD ya yi maraba da nada firaiminista da kuma sanarwar da aka fitar game da ranar da za'a gudanar da zaben majalisar dokokin kasar Guinea-Bissau.

Francisco Tenya, mataimakin wakilin din din din na kasar Peru a MDD, ya shedawa 'yan jaridu cewa, mambobin kwamitin sun yi na'am da nada Aristides Gomes, a matsayin sabon firaiministan kasar bisa ga irin matsayar da aka cimma tsakanin masu ruwa da tsaki a harkokin siyasar kasar, da kuma ayyana ranar 18 ga watan Nuwamba a matsayin ranar gudanar da zaben 'yan majalisar dokokin kasar.

Mambobin kwamitin tsaron MDDr sun jaddada muhimmancin kafa gwamnatin hadin kan kasar, da dawowar majalisar dokokin kasar bakin aikinta, da kuma shirya sahihin zaben a kan lokaci, in ji Tenya, wanda kasarsa ta karbi shugabancin kwamitin tsaron MDDr a watan Afrilu, bayan wata tattaunawar sirri da kwamitin ya shirya.

Mambobin kwamitin sun kuma bukaci a kara azama wajen aiwatar da yarjejejniyar Conakry, da aiwatar da matakai 6 da kungiyar hada kan tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma (Ecowas) ya shirya.

Mambobin sun nuna goyon bayansu ga yunkurin Ecowas na lalibo hanyoyin kawo karshen dambarwar siyasar kasar ta yammacin Afrika, wanda ya barke tun bayan da shugaba Jose Mario Vaz, ya kori tsohon firaiministan kasar Domingos Simoes Pereira a watan Agustan shekarar 2015.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China