Shugaban kasar Guinea-Bissau Jose Mario Vaz ya sanar a ranar Litinin, a cikin wani jawabi zuwa ga 'yan kasarsa, da rushe gwamnatin firaminista Baciro Dja, da nada wani sabon firaministan da zai samu amincewar kowa cikin sauri.
Wannan sabon faraminista, a cewar shugaban kasar, za a daura masa nauyin kafa wata gwamnatin hadaka, kamar yadda yarjejeniyar Conakry ta tanada, domin fitar da Guinea-Bissau daga ricikin siyasa da zaman zullumi na fiye da shekara guda.
A cikin jawabin nasa, shugaba Vaz ya bayyana cewa, ya dauki wadannan matakai bayan da ya tuntubi jam'iyyun siyasa da kwamitin kasa, wato wata hukumar tuntubar juna dake hade da fadarsa. (Maman Ada)