Jami'in wanda ya bayyana hakan cikin wani sharhin da ya rubuta mai taken "An yi maraba da dakatar da takaddamar Sin da Amurka na sanyawa juna haraji" wanda aka wallafa jiya Talata a jaridar nan ta San Francisco Chronicle, ya ce, matakin da kasashen biyu suka dauka labari ne mai dadin ji ga tattalin arziki game da kasuwannin duniya. Shugabannin kasashen Sin da Amurka dai sun gana tare da cin abincin dare a gefen taron kolin kungiyar G20 da ya gudana a kasar Argentina.
A yayin da zaman cin abincin daren, shugaba Xi Jinping na kasar Sin da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump sun amince ba za su kara sanyawa juna wani sabon haraji ba. Ya kamata a ce kasashen biyu za su magance bambance-bamnbancen dake tsakaninsu, duba da yadda sassan biyu ke amfana da juna a fannin tattalin arziki.
Jami'in na kasar Sin ya kara da cewa, galibin Amurkawa da ya tattauna da su, suna fatan za a hanzarta kawo karshen takaddamar cinikayyar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma magance kara kawo wa kamfanonin Amurka illa sakamakon harajin.(Ibrahim)