in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Turai da Indiya da Japan sun soki matakan da Amurka ke dauka na bada kariya ga harkokin kasuwanci
2018-12-20 14:07:11 cri
Kungiyar kasuwanci ta duniya WTO, ta kammala aikin binciken manufofin kasuwanci na gwamnatin Amurka karo na 14 a jiya Laraba. A wajen taruka biyu da aka yi a ranar 17 da ranar 19 ga wata, wasu kasashen duniya ciki har da Sin da Japan da Indiya, gami da kungiyar tarayyar Turai wato EU, sun soki matakan gwamnatin Amurka na bada kariya ga harkokin cinikayya, ciki har da sanya harajin kwastam kan karafa da samholo, da kuma hana zabar membobin kungiyar gabatar da kararraki.

A cikin shekarar da ta gabata, Amurka ta yi yunkurin nuna fin karfinta a duk duniya, da aiwatar da matakan bada kariya ga harkokin kasuwanci, al'amarin da ya sa binciken manufofin kasuwancin kasar da aka yi a wannan karo ya jawo hankali sosai, har ma kasashe membobin WTO sama da 40 suka aza wa Amurka tambayoyi fiye da 1700.

Game da shakkun da ake nuna mata, zaunannen jakadan Amurka dake WTO Dennis Shea ya yi jawabi sau biyu, inda ya yi yunkurin dora laifin kan kasar Sin, da nemowa Amurka hujja ta bada kariya ga harkokin kasuwanci. A cikin jawabin da ya gabatar a jiya Laraba, Dennis Shea ya ce, EU na da rashin fahimta game da zargin da aka yiwa Amurka, na cewa ita ce ta haddasa rikicin tsarin kasancewar bangarori daban-daban wajen yin cinikayya a duniya, kuma rikicin ya kunno kai ne sakamakon rashin daidaito tsakanin kasar Sin da tsarin yin cinikayyar duniya.

Mataimakin kwamishinan kula da harkokin yin shawarwari na sashin kasuwancin duniya na ma'aikatar kasuwancin kasar Sin, Hu Yingzhi ya karyata zargin da ake wa kasar Sin, inda ya jaddada cewa, Amurka ce aka gudanar da bincike a kanta, ba kasar Sin ba. Kasar Sin ta ki yarda da duk wani yunkuri da aka yi na maida ta tamkar hujja ta nuna fin karfi a duniya, da bada kariya ga harkokin kasuwanci, da kuma dora mata laifin ba tare da tushe ba ko kadan.

Hu ya kara da cewa, Amurka kasa ce mafi karfin tattalin arziki a duk fadin duniya a halin yanzu, wadda ta zama babbar kasa dake cin moriya sosai daga tsarin tattalin arzikin duniya, da tsarin kasancewar bangarori daban-daban wajen yin cinikayya. Kasar Sin na fatan Amurka za ta kara fahimtar wannan batu, maimako ta dorawa sauran kasashe laifin.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China