in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 3 sun mutu yayin harin da aka kai ofishin 'yan sandan Nijar
2019-02-14 10:39:26 cri

Wasu dakarun da ba a san ko su waye ba, sun kai hari kan wani ofishin 'yan sandan jihar Dosso dake yammacin kasar Nijar, al'amarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 3.

Hukumar kiyaye tsaron kasar ta bayyana cewa, dakarun sun yi amfani da na'urar harba roka yayin da suka kai hari dakin adana kayayyaki na ofishin 'yan sandan, haka kuma sun kone gawarwakin 'yan sanda biyu kafin tserewarsu.

Yanzu hukumar 'yan sandan kasar ta riga ta tura jami'an tsaro domin neman wadanda suka kai harin.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China