in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Niger: An hallaka sojoji biyu a harin ta'addanci
2018-07-02 09:45:04 cri

Wata majiyar jami'an tsaro ta tabbatar da cewa, an kashe akalla sojojin jamhuriyar Nijer biyu a wani harin da mayakan 'yan ta'adda na Boko Haram suka kaddamar a daren ranar Asabar a kan iyakar kasar da Najeriya.

Harin ya faru ne a yankin kudu maso yammacin yankin N'Guigmi dake jihar Diffa, kana wasu sojoji da dama sun jikkata, kuma hare haren sun ci gaba har zuwa safiyar ranar Lahadi, kamar yadda majiyar ta tabbatar da hakan.

Harin na Nijer dai ya faru ne a daidai lokacin da aka shirya taron ganawa tsakanin shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da shugabannin kungiyar G5 na yankin Sahel a Nouakchott, babban birnin kasar Mauritania, a gefen taron kolin kungiyar tarayyar Afrika AU dake gudana a halin yanzu.

Ana sa ran shugabannin za su tattauna game da halin da ake ciki game da yanayin tsaro a shiyyar, ciki har da batun aikin tabbatar da tsaro na hadin gwiwar kasashen G5-Sahel.

Shekaru sama da 3 da suka gabata, yankuna da dama a jihar Diffa, da kuma yankunan dake makwabtaka da Najeriya, sun sha fama da hare haren mayakan 'yan ta'adda na Boko Haram, wadanda suka yi sanadiyyar rayukan daruruwan fararen hula da sojoji, kana suka yi sanadiyyar raba wasu dubban mutane da matsugunansu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China