in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar wajen Sin: Bai dace ba Amurka ta danne kamfanonin kasar Sin
2019-02-13 19:36:04 cri

Yau Laraba kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing cewa, kasar Sin ta mai da hankali sosai kan maganganun da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya yi yayin da yake ziyarar aiki a kasashen dake tsakiya da kuma gabashin nahiyar Turai, saboda duk da cewa, Amurka ba ta gabatar da wasu shaidu ba, amma tana zargin kamfanonin kasar Sin kamar yadda take so, tana kuma danne ci gaban kamfanonin ta hanyar yin amfani da karfinta, kuma hakan ko kadan bai dace ba saboda hakan ba adalci ko da'a ba ne.

Bayanai na nuna cewa, bayan da Pompeo ya gargadi takwaransa na kasar Hungary cewa, kada kasar ta girke na'urorin sadarwa na kamfanin Huawei na kasar Sin a kasar, haka kuma Pompeo ya ci gaba da bayyanawa yayin da yake ziyara a kasar Slovakiya cewa, dole ne Slovakiya ta fahimci cewa, kila kasar Sin za ta jagoranci tsarin siyasar kasar ta hanyar tattalin arziki ko wasu hanyoyi, kana ya bayyana cewa, Amurka na fatan aminiyarta wato Slovakiya ta kara sanin cewa, sayen hajojin kasar Sin yana da hadari. Ban da wannan, yayin da yake ziyarar aiki a kasar Poland, Pompeo ya bayyana cewa, idan Poland ta daina yin hadin gwiwa da kasar Sin, to Amurka za ta gina sansanin soji a kasar cikin sauki. Game da wannan, madam Hua Chunying ta bayyana cewa, ba zai yiyu ba kasar Sin ta tsoma baki a cikin harkokin gidan wasu kasashe, balle ma ta jagoranci tsarin siyasar wata kasa daban.

Hua ta kara da cewa, kasar Sin tana fatan Amurka da sauran kasashen da abin ya shafa za su martaba ka'idar kasuwa ta yin takara bisa tushen adalci da walwala, ta yadda za a kiyaye yanayin kasuwa cikin adalci.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China