in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU na sa ran yankin ciniki cikin 'yanci na Afrika zai fara aiki cikin Yuli
2019-02-11 10:21:26 cri

Kwamishinan harkokin ciniki da masana'antu na tarayyar Afrika AU, Albert Muchanga, ya ce yana sa ran yankin ciniki cikin 'yanci na nahiyar, zai fara aiki a hukumance a watan Yulin bana.

Da yake jawabi ga wani taron manema labarai da aka yi a gefen babban taron kungiyar na 32, da ya gudana a Addis Ababa na Habasha, Albert Muchanga ya ce ana sa ran kaddamar da yankin ne yayin taron kungiyar da za a yi a birnin Niamey na kasar Niger cikin watan Yuli.

Kwamishinan ya ce, yanzu, akwai kasashen nahiyar 12 da suka amince da kunshin yarjejeniyar kafa yankin, kuma kafin karshen taron kungiyar, suna sa ran wasu karin kasashe 2 za su amince.

Ya ce, ya zuwa ranar 21 ga watan Maris na bana, za a cika shekara guda da kaddamar da yankin, kuma suna sa ran za su cike adadin da aka kayyade na kasashe mambobi 21 da ake bukata kafin yarjejeniyar ciniki cikin 'yancin ta fara aiki.

Har ila yau, ya ce AU na sa ran kasashe mambobinta za su fara cire shingayen cinikayya a tsakaninsu tare da rage kudaden haraji da kuma lalubo dabarun bibiyar shingayen da ba na haraji ba na wasu kasashe.

Albert Muchanga, ya ce AU na kokarin fito da mizanin ingancin kayayyaki da wasu sauran ka'idojin cinikayya da za su ja hankalin manyan kasashe kamar Nijeriya, wadda ta kauracewa amincewa yarjejeniyar.

Tarayyar Afrika dai na fatan yankin ciniki cikin 'yanci na Afrika, zai bunkasa ci gaban bangarori masu zaman kansu a nahiyar, sannan za ta yi aiki wajen kafa kungiyar masana'antu, domin sa ran fara aiki da yankin a bana. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China