in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar wajen Sin: Sin tana fatan Amurka za ta dauki matakin da ya dace kan batun Taiwan
2019-01-25 20:14:18 cri

Yau yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta bayyana cewa, batun Taiwan yana da muhimmanci matuka ga alakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Amurka, a don haka kasar Sin ke bukatar Amurka da ta bi ka'idar kasar Sin daya kacal a duniya, da ka'idojin da Sin da Amurka suka tsara, a cikin hadaddun rahotanni uku. Haka kuma ta dauki matakin da ya dace, yayin daidaita abubuwan da ke shafar yankin Taiwan na kasar Sin, in ba haka ba, za ta lalata alakar dake tsakanin kasashen biyu, tare kuma da kawo illa ga kwanciyar hankali a zirin Taiwan.

An ce, jiragen ruwan yakin Amurka guda biyu, sun yi zirga zirga a zirin Taiwan, kuma sun bayyana cewa, sojojin Amurka za su ci gaba da yin zirga zirga a sararin sama, ko kan ruwan teku a ko ina a fadin duniya, bisa amincewar dokar kasashen duniya. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China