in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar wajen Sin ta karyata zargin shugabar yankin Taiwan game da kulla huldar diplomasiyya da kudi
2018-05-29 18:50:39 cri

A yau Talata yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana cewa, zargin da shugabar yankin Taiwan na kasar Sin Cai Yingwen ta yi, game cewa babban yankin kasar Sin yana kulla huldar diplomasiyya tsakaninsa da sauran kasashe ta hanyar bayar da kudi, ba shi da tushe ko kadan, kuma zargi ne maras dalili.

Hua Chunying ta kara da cewa, kasar Sin daya ce tak a duniya, kana gwamnatin jamhuriyar jama'ar kasar Sin, ita ce halastacciyar gwamnati daya kadai dake wakiltar daukacin al'ummun kasar ta Sin, yayin da kuma Taiwan ke kasancewa daya daga yankunan kasar Sin, wanda ba za a iya raba shi daga kasar Sin ba.

Jami'ar ta ce wannan kuduri baya ga amincewa da yake da shi a MDD, ya kuma samu amincewa a wajen yawancin kasashen duniya baki daya. Kana har kullum gwamnatin kasar Sin na nacewa ga bin ka'idar nan ta kasa Sin daya tak a duniya, ba kuma zai yiyu a canja wannan matsayi ba, a baya, ko a yanzu, ko ma a nan gaba.

Hua Chunying ta yi nuni da cewa, kasar Burkinafaso ta yanke huldar diplomasiyya da yankin Taiwan, ta kuma maida huldar diplomasiyyar ta da kasar Sin, don haka ana iya cewa, kudurin siyasar da gwamnatin Burkinafaso ta tsaida na cike da hikima, ya kuma dace da dokar kasa da kasa, da ka'idar huldar kasa da kasa, haka kuma ya dace da babbar moriyar al'ummun kasashen biyu, da ci gaban zamanin da muke ciki, a don haka kudurin ya samu goyon baya daga sassa daban daban a kasar ta Burkinafaso.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China