in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi da Trump sun aikewa juna sakonnin murnar cika shekaru 40 da kulla huldar diflomasiya tsakanin Sin da Amurka
2019-01-01 14:50:31 cri

A yau ne shugaba Xi Jinping na kasar Sin da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump suka aikewa juna sakonnin murnar cika shekaru 40 da kulla huldar diflomasiya tsakanin kasashensu.

A cikin sakonsa, shugaba Xi ya ce alakar kasashen biyu ta fuskanci kwangaba kwanbaya, an kuma samu ci gaban tarihi cikin shekaru 40 din da suka gabata, lamarin da ya haifar da tarin moriya ga al'ummomin kasashen biyu, baya ga gagarumar gudummawa da alakar ta ba da ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.

Shugaba Xi ya ce, tarihi ya nuna cewa, hadin gwiwa ita ce hanya mafi dacewa ga bangarorin biyu. A halin yanzu alakar Sin da Amurka tana cikin muhimmin mataki.

A nasa bangare, shugaba Trump ya ce, ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2019, shekaru 40 ke nan da kulla huldar diflamosiya tsakanin kasashen biyu. Kuma a cikin wadannan shekaru 40 da suka gabata, an cimma manyan nasarori yayin alakar bangarorin biyu.

Trump ya kara da cewa, zai kara mayar da hankali wajen inganta alakar dake tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare, yana mai cewa, abokantakar dake tsakaninsa da shugaba Xi, ta shinfida wani harsashe kan manyan nasarori da kasashen biyu za su cimma cikin shekaru masu zuwa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China