in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta karfafa matakan kare kayayyakin al'adu
2019-01-09 10:00:29 cri

Shugaban hukumar kare kayayyakin al'adu ta kasar Sin Liu Yuzhu, ya bayyana cewa, a sabuwar shekarar 2019 hukumarsa za ta tsara wasu matakai na kara kare kayayyakin al'adun gargajiya.

Shugaban wanda ya bayyana hakan yayin wani taron shugabannin sassan kula da kayayyakin al'adun gargajiya na kasar, ya jaddada muhimmancin daukar irin wannan mataki.

Hukumar ta kuma lura da cewa, kananan hukumomi a wasu lardunan kasar sun gaza bayyana yawan yankunan kare irin wadannan kayayyakin gargajiya da suke da su da ma gina yankunan tsaro.

Don haka Mr Liu ya ba da umarnin ci gaba da sanya ido kan kayayyakin al'adun gargajiya, da yaki da masu nasaba da ayyukan da suka shafi kayayyakin al'adun gargajiya, da kara inganta matakan tsaro, da kara ba da taimakon dabaru don kare kayayyakin al'adu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China