in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: Sassan watsa bayanai da nishadantarwa na ci gaba da samun tagomashi
2018-06-07 10:35:24 cri
Wani rahoto da aka fitar game ci gaba da ake samu a fannonin watsa bayanai da nishadantarwa na kasar Sin ya nuna cewa, sassan 2 na samun tagomashi, kana akwai hasashen cewa, ci gaban su zai dore cikin shekaru 5 dake tafe.

Rahoton wanda wani kamfanin lissafin kudade da kadarori mai zaman kan sa ya fitar a jiya Laraba, ya nuna cewa sassan biyu za su samu ci gaba da ya kai kaso 7.2 bisa dari a duk shekara, tun daga shekarar bana zuwa shekarar 2022. Kana adadin kudade da sassan biyu za su kunsa za su kai dalar Amurka biliyan 343.

Hakan dai na nuna irin ci gaba da fannonin watsa bayanai da nishadantarwa na kasar Sin za su samu, wanda ya zarce matsakaicin ci gaba da sauran kasashen duniya ke samu a fannonin, wanda bai wuce kaso 4.4 bisa dari ba.

Faya fayan bidiyo da ake dorawa kan yanar gizo, da tallace tallace, da faya fayan bidiyo na wasanni, su ke kan gaba wajen samun bunkasuwa, wadanda bisa kididdiga ke samun ci gaba na kaso 16.3%, da kaso 11.8% da kuma kaso 9.7%.

Rahoton ya kara da cewa, yanar gizo ko Internet, za ta ci gaba da zama a sahun gaba a fannin bunkasa fannonin biyu, a gabar da wayoyin salula masu dauke da nayar gizon ke kara samar da hidimomi, da sabbin fasahohi masu haifar da sabbin damammaki ga mutane.

Rahoton ya kuma kara da cewa, fannonin watsa bayanai da nishadantarwa na kasar Sin bai fuskanci kalubale ba, a lokutan da ake tsaka da fuskantar komadar tattalin arziki, maimakon hakan ma sassan biyu dagawa suka yi, daga matsayin kananan fannoni dake samar da hidimomi, zuwa manyan masana'antu dake ba da muhimman hidimomi ga al'umma. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China