in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan wadanda suka mutu a ambaliyar ruwan tsunami a Indonesia ya karu zuwa 373
2018-12-25 10:57:47 cri

A yayin da ake ci gaba da gudanar da aikin ceto duk da irin rashin kyawun yanayi da lalacewar hanyoyin shiga wuraren da bala'in ya shafa, an tabbatar da cewa, adadin mutanen da suka rasu a sakamakon ibtila'in tsunamin wanda ya afkawa yankin Sunda Strait dake yammacin kasar Indonesia ya karu zuwa mutane 373, yayin da adadin wadanda suka jikkata ya kai 1,459.

Daruruwan jami'an sojoji, 'yan sanda, ma'aikatan ceto, da masu aikin sa-kai ne suke ci gaba da gudanar da aikin bincike da kuma ceton mutanen da bala'in ya rutsa da su a yankunan da ambaliyar ruwan ta shafa dake gabar tekun yammacin Java da kudancin tsibirin Sumatra, wadanda a ranar Asabar suka gamu da mummunar ambaliyar ruwan tsunami bayan zaftarewar laka da aka samu a sanadiyyar aman wuta da aka samu a yankin Anak Krakatau wanda aka shafe tsawon wata guda ana fama da matsalar.

Masu aikin ceto dauke da manyan injuna da na'urori suna ci gaba da kutsawa wuraren da ibtila'in ya shafa, inda suke ci gaba da zakulo gawarwakin wadanda bala'in ya rutsa da su.

"Bisa gudanar da aiki tukuru tare da taimakon manyan injuna, masu aikin ceton sun samu nasarar kutsawa yankunan da bala'in ya fi kamari wadanda a lokutan baya babu damar shiga wuraren," kakakin hukumar kai dauki gaggawa na kasar Sutopo Purwo Nugroho ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China