in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin wadanda suka mutu sanadiyyar girgizar kasa a Indonesia ya karu zuwa 259
2018-08-10 09:58:03 cri

Adadin wadanda suka mutu sanadiyyar girgizar kasar da ta aukawa tsibirin Lombok dake yammacin lardin Nusa Tenggara na Indonesia, ya kai 259 ya zuwa jiya Alhamis.

Hukumomin da suka bayyana adadin, sun ce akwai yiwuwar ya karu yayin da ake ci gaba da aikin ceto wadanda ke karkashin gine-ginen da suka rushe.

Bayan wani taro da ya samu halartar wakilan hukumar tunkarar iftila'i ta kasar da sojoji da 'yan sanda da wakilan hukumar aikin ceto, wanda ya gudana a cibiyar aikin ceto dake gundumar Tanjung na arewacin Lombok, kakakin hukumar tunkarar iftila'i ta kasar Sutopo Purwo Nugroho, ya ce wakilan hukumomin da suka halarci taron, sun amince da wancan adadi na wadanda suka mutu a hukumance.

Ya ce, an kara matse kaimin ci gaba da kokarin binciko sauran gawarwaki daga karkashin baraguzan gine-ginen da suka rushe.

Ya kara da cewa, mutane 1,033 ne suka jikkata yayin da 270,168 suka rasa matsugunansu, wadanda a yanzu ke samun mafaka a wurare daban-daban.

Har ila yau, ya ce an kara zage damtse wajen ganin an kai kayayyakin agaji ga wadanda suka rasa matsugunansu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China