in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude gasar wasannin Asiya a Jakartan Indonesia
2018-08-19 16:38:59 cri

A daren jiya Asabar, aka bude bikin gasar wasannin Asiya karo na 18, a daidai lokacin da aka gudanar da wani kasaitaccen biki a Jakarta, babban birnin kasar Indonesia.

Kwana guda bayan gudanar da bikin cika shekaru 73 da samun 'yancin kan kasar Indonesia, shugaban kasar ta Indonesia Joko Widodo ya jagoranci bikin bude gasar wasannin a babban filin taro na Gelora Bung Karno bayan jawabin da shugaban majalisar shirya wasanni ta OCA Sheikh Ahmad Al-Fahad Al-Sabah ya gabatar.

Wakiliyar musamman ta shugaban kasar Sin Xi Jinping, kana mataimakiyar firaiministan Sin Sun Chunlan ta halarci bikin.

Gasar wasannin ta Asiya, ta ja hankalin 'yan wasa sama da 10,000, za'a gudanar da wasannin zuwa ranar 2 ga watan Satumba. Wannan shi ne karo na biyu da Jakarta take karbar bakuncin wasannin na Asiya. An kaddamar da wasannin a karon farko ne a New Delhi, na kasar India a shekarar 1951.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China