181218-Xi-Jinping-Kande
|
A ranar 18 ga watan Disamban shekarar 1978, an kira taro na uku na dukkan wakilan kwamitin tsakiya na 11 na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, inda aka tsai da kudurin aiwatar da manufar bude kofa ga waje da yin kwaskwarima a gida, da zamanintar da al'ummar Sin mai tsarin gurguzu. A cikin wadannan shekaru 40 da suka gabata, jimillar GDP ta kasar Sin ta karu daga kashi 1.8 cikin dari zuwa kashi 15.2 cikin dari bisa ta duk duniya. Bugu da kari kuma, yawan gudummawar da kasar Sin ta ba duniya ta fuskar tattalin arziki ya zarce 30% a jerin shekaru da dama.
A yayin taron taya murnar cika shekaru 40 da kaddamar da manufar bude kofa ga waje da yin kwaskwarima a gida da aka yi a safiyar yau Talata a birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da muhimmin jawabi, inda ya bayyana cewa,
"Manufar bude kofa ga waje da yin kwaskwarima a gida, wani muhimmin kuduri ne da jam'iyyarmu ta tsayar, wanda ya shaida nasarar da jam'iyyarmu ta samu daga tsarinta a rubuce zuwa hakikanin abu a zahiri. Haka kuma manufar wani babban juyin juya hali ne ga tarihin ci gaban al'ummar Sin, wanda ya sa kaimi ga babban ci gaban sha'anin gurguzu da ke da halin musamman na Sin."
Shugaba Xi ya waiwayi sakamako da fasahohin da kasar Sin ta samu a cikin wadannan shekaru 40 da suka wuce, bayan da aka fara aiwatar da manufar, inda ya jaddada cewa,
"Nasarorin da aka samu a cikin wadannan shekaru 40 da suka wuce ba abu ne da wani ya ba mu ba, a maimakon hakan, an same su ne bisa kokari, basira da ma jaruntaka da Sinawa ke da shi. Mun yi amfani da shekaru gomai ne kawai wajen kammala aikin masana'antu wanda kasashe masu sukuni suka kwashe shekaru daruruwa suna yi. A wajenmu Sinawa, mun canja abu maras yiyuwa zuwa na gaske. Lallai muna alfahari da Sinawa da suka yi abubuwa masu ban al'ajabi haka."
A waje daya kuma, Xi ya jaddada cewa, bunkasuwar kasar Sin na dogaro da duniya, kana wadatuwar duniya ma na bukatar kasar Sin. Wajibi ne kasar Sin ta tsaya kan habaka bude kofa ga kasashen ketare, da inganta kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil adama.
"Za mu girmama hakkin jama'ar kasashe daban daban, na zabar hanyar neman ci gaba mai dacewa, da kiyaye adalci na tsarin duniya, da karfafa kwarin gwiwa wajen kafa huldar demokuradiyya a tsakanin kasa da kasa. Kana muna adawa da tilastawa wasu amince da ra'ayin wani, da kutsa kai cikin harkokin cikin gida na sauran kasashe, da wulakanta marasa karfi. Baya ga haka, za mu taka rawa bisa matsayinmu na wata babbar kasa, da goyon bayan ci gaban kasashe masu tasowa, da sa himma wajen shiga ayyukan yin kwaskwarima da raya tsarin gudanar da harkokin duniya, bisa aniyar neman samun zaman lafiya mai dorewa, da tsaro a ko ina, da wadatar kowa, da bude kofa, da hakuri da juna, da ma muhalli mai tsabta a duniya. Kana muna goyon bayan tsarin cinikayya na bangarori da dama, da inganta samar da sauki wajen yin cinikayya cikin 'yanci, domin kara azama ga dunkulewar tattalin arzikin duniya guri daya."
Baya ga haka Xi ya furta cewa, kasar Sin za ta dora muhimmanci sosai kan shawarar "Ziri daya da hanya daya", a yayin kokarin da take yi tare da bangarori daban daban wajen kafa sabon dandalin hadin kan kasa da kasa, domin ba da tallafi ga ci gaban duniya baki daya. Ko kadan kasar Sin ba za ta nemi raya kanta ta hanyar cin moriyar sauran kasashe ba, amma kuma ba za ta yi watsi da halartattun muradunta ba. Haka zakila, kasar Sin na bin manufar tsaron kai, kana ci gaban kasar Sin ba zai kai wa saura barazana ko kadan ba. Komin bunkasuwarta, kasar Sin ba za ta nemi mallakar duniya ba.(Kande Gao)