in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sharhi: Fahimci kasar Sin bisa wasu tambayoyi 3
2018-12-17 20:09:01 cri

A bana za a cika shekaru 40 da fara aiwatar da manufar kasar Sin ta yin gyare-gyare a gida a bude kofa ga kasashen waje. A wannan lokaci mai ma'ana, kasashen yammacin duniya sun kara mai da hankali kan wasu tambayoyi game da kasar Sin, irinsu "Mene ne makomar kasar Sin?", "Sin wata abokiya ce ko kuma kasa ce da za a yi takara da ita?", "Kasar Sin na samar da damammaki ko kuma kalubaloli?" Bisa wannan yanayi ne, aka bude wani taron karawa juna sani mai taken "Fahimci kasar Sin" a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, a ranar Lahadi da ta gabata, taron dake da ma'ana matuka.

Taron "Fahimci kasar Sin" an taba gudanar da shi a shekarar 2013 da 2015, duk a birnin Beijing, tare da nufin baiwa kasashen duniya damar kara fahimtar kasar Sin, da karfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen waje. Taron na wannan karo ya samu halartar mutane kimanin 600, ciki har da fitattun 'yan siyasa, da shugabannin kamfanoni kusan 40. Ban da haka kuma, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika da sakon taya murna ga taron, inda ya jaddada aniyyar kasar Sin ta kara zurfafa gyare-gyare, gami da bude kofar kasar ga kasashen waje. A cewar shugaban, kasar Sin za ta ci gaba da aiwatar da sabbin manufofin raya kasa, don tabbatar da ci gaban tattalin arzikin kasar, da ingancinsa, ta yadda za a samar da karin damammakin hadin gwiwa ga kasashe daban daban. Bisa wadannan jimloli, shugaban ya amsa tambayoyin da kasashen dake yammacin duniya suka yi, sa'an nan ya karfafawa masu halartar taron gwiwa, domin su tattauna bisa babban taken taron na "Sabbin matakan ciyar da kasar Sin gaba, da sabbin damammakin hadin gwiwa da za a samu a duniya".

Kamar yadda ake tunani kan wasu tambayoyi masu sarkakiya dangane da zaman rayuwar dan Adam, batun dake da alaka da kasar Sin da gamayyar kasa da kasa, musamman ma kasashen yammacin duniya suka yi, za a iya takaita su zuwa tambayoyi 3, wato: Wace irin kasa ce kasar Sin? A wane yanki take? Kuma ina ta dosa? Dangane da wadannan tambayoyi, baki masu halartar taron "Fahimci kasar Sin" na wannan karo, sun ba da nasu amsoshin, bisa la'akari da tarihi da makomar manufar yin gyare-gyare da bude kofa ta kasar Sin.

Game da tambaya ta farko, wakilin ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar JSK Yang Jiechi ya bayyana cewa, gamayyar kasa da kasa za su iya kara fahimtar kasar Sin a fannoni daban daban, Kaman Sin tana tsayawa tsayin daka wajen neman bunkasuwa cikin zaman lafiya, inganta hadin gwiwar dake tsakanin bangarori daban daban domin cimma moriyar juna, kuma ta kan nuna adalci, yayin da dukufa wajen karfafa aikin kara tsaro da kuma nuna fahimtar juna da dai sauransu.

A nasa bangare kuma, shugaban ofishin watsa labarai na gwamnatin kasar Sin Xu Lin ya nuna cewa, manufar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje yana cikin babban burin kasar Sin, wadda take da muhimmanci wajen daidaita makomar kasar.

Game da tambaya ta biyu, shugaban kungiyar nazarin harkokin sabuntawa da ci gaban kasar Sin Zheng Bijian ya bayyana cewa, a daya bangare, cikin shekaru 40 da suka gabata, GDP na kasar Sin ya karu daga Yuan biliyan 360 a shekarar 1978 zuwa Yuan biliyan dubu 82 ko fiye a shekarar 2017, amma matsakaicin GDP na kowane Basine yana kan matsayi na 70 kawai a duk fadin duniya. Haka kuma, kasar Sin, kasa ce dake sahun gaba a duniya a fannin kirkire-kirkire, amma matsayin kasar a wannan fanni bai kai matsakacin matsayin duniya ba. Lamarin da ya nuna cewa, ya kamata a ci gaba da yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje bisa sakamakon da aka samu cikin shekaru 40 da suka gabata, kuma mu ci gaba da aiwatar da manufar bisa burinmu na warware babbar matsala ta fuskar zaman takewar al'umma a halin yanzu.

Kuma mene ne burin kasar Sin a nan gaba? Mahalarta taron suna ganin cewa, shi ne burin neman bunkasuwar tattalin arziki da zaman takewar al'umma da aka gabatar yayin cikakken zaman taron wakilan JKS karo na 19, wanda ya hada da, samar da al'umma mai dauwamammen ci gaba a fannonin siyasa, tattalin arziki da al'adu nan da shekarar 2020, da kuma kyautata tsarin gurguzu na kasar zuwa wani tsarin da babu kamarsa a duniya nan da shekarar 2035, sa'an nan kuma, kafa wata kasa mai tsarin gurguzu dake kan gaba a duniya nan da tsakiyar wannan karni.

Mr. Zheng Bijian yana ganin cewa, wannan ba wani buri ne da kasar Sin take son yin mulkin danniya a duk duniya ba, wani buri ne da kasar Sin take son bunkasa kanta kawai. A lokacin da take kokarin cimma wannan buri, karfin kasuwa da na kirkiro sabbin fasahohin zamani da kasar Sin take da su za su kasance a wani matsayin dake jawo hankalin mutane sosai. A waje daya, tabbas ne al'ummomin Sin da na sauran kasashen duniya za su yi kokarin kafa wata al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama da kuma cin gajiya tare cikin hadin gwiwa.

James Gordon Brown, tsohon firaministan kasar Burtaniya ya amince da wadannan ra'ayoyi. A jawabin da ya gabatar, Mr. Gordon Brown ya nuna cewa, kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama ba wani tunani ne kawai ba, tabbas za a tabbatar da ganin ya tabbata nan ba da dadewa ba. Ya kuma yi kira a kafa wata al'ummar da ke hade da juna. Mr. Brown ya kuma bayyana cewa, yanzu an fi bukatar yin hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya ta yadda za a iya kawar da ra'ayin 'yan mazan jiya.

Ana samun adalci ne sakamakon fahimtar juna. A wannan muhimmin lokaci na cika shekaru 40 da kasar Sin ta kaddamar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofarta ga ketare, muhimman 'yan siyasa da masu nazari da tsara manyan manufofi da masu tafiyar da masana'antu wadanda suka fito daga fadin duniya sun yi kwanaki 3 suna nazarin sabon karfin kara ciyar da kasar Sin gaba bisa manufofin neman bunkasuwa na shiyya-shiyya, da kirkiro sabbin fasahohin zamani da sabunta masana'antu da kuma bunkasa tsarin hada-hadar kudi na zamani da dai makamatansu, sannan suna kokarin samun sabuwar damar yin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa bisa sabuwar huldar dake tsakanin kasa da kasa da kokarin tabbatar da kwanciyar hankali a yankuna daban daban da kuma shawarar bunkasa "ziri daya da hanya daya". Wannan gudummawa da suka bayar, ba ma kawai zai taimakawa al'ummomin yammacin duniya su kara fahimtar kasar Sin ba, har ma zai amfana wa duk duniya ta kara cin gajiya. (Masu Fassarawa: Sanusi Chen, Bello Wang, Maryam Yang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China