181217-tsohon-shugaban-mozambick-na-ga-sakamakon-gyaran-fuska-da-bude-kofa-a-sin-da-idona.m4a
|
Kwanan baya a unguwar Conghua ta birnin Guangzhou dake lardin Guandong a kudancin kasar Sin, an shirya dandalin kasa da kasa na Imperial Springs na shekarar 2018, inda mahalarta sama da 200 suka gabatar da ra'ayoyinsu, kan babban taken dandalin wato "gyaran fuska da bude kofa, da hadin gwiwa da kuma samun moriya tare".
Tsohon shugaban kasar Mozambick Joaquim Alberto Chissano na cikin mahalarta dandalin, ya kuma bayyana cewa, ya ga sakamakon da kasar Sin ta samu a zahiri, tun bayan da ta fara aiwatar da manufar gyaran fuska da bude kofa kafin shekaru 40 da suka gaba.
Kungiyar sada zumunta ga kasashen waje ta kasar Sin, da kungiyar sada zumunta dake tsakanin Sin da Autralia ne suka kafa dandalin kasa da kasa na Imperial Springs cikin hadin gwiwa a shekarar 2014, inda a kan gayyaci shahararrun tsoffin 'yan siyasa, da masana, da 'yan kasuwa domin su halarci dandalin. Babban taken dandalin na bana shi ne "gyaran fuska da bude kofa, da hadin gwiwa da kuma samun moriya tare".
Bana ake cika shekaru 40 da fara aiwatar da manufar gyaran fuska a gida da bude kofa ga ketare a nan kasar Sin. A don haka mahalartan dandalin na kasa da kasa na Imperial Springs, suka gabatar da ra'ayoyinsu daban daban kan sakamakon da kasar Sin ta samu a cikin wadannan shekaru 40 da suka gabata, inda tsohon shugaban kasar Mozambick Joaquim Alberto Chissano ya bayyana cewa, ya ga sakamakon da kasar Sin ta samu da idonsa.
Kasashen nan biyu wato Sin da Mozambick sun daddale huldar diplomasiya dake tsakaninsu ne a shekarar 1975, a wancan lokaci, Chissano ya ziyarci kasar Sin a karo na farko bisa matsayinsa na ministan harkokin wajen kasarsa, ya ce, ba zai manta da kekunan da ake hawa a titunan biranen kasar Sin ba, yana mai cewa, "A wancan lokaci, keken hawa ya fi muhimmanci a rayuwar yau da kullum na Sinawa; A Beijing, ko a Shanghai, ko kuma a Xi'an, ko ina ana iya ganin Sinawa a kan kekuna, kana Sinawa suna jigilar kayayyakin su a kan kekune. Misali kai marasa lafiya zuwa asibiti, ko jigilar kayan abincin da suka saya a kanti zuwa gida. To amma yanzu an fi amfani da motoci, yayin da keken hawa ya zama abun motsa jiki kawai."
Bisa matsayinsa na tsohon shugaban kasar ta Mozambick, Chissano ya ce ya ga manyan sauye-sauyen da suka faru a kasar Sin da idonsa, ya ce, "Yanzu kasar Sin ta riga ta kasance kasa mafi saurin ci gaban tattalin arziki ta biyu a fadin duniya, dalilin da ya sa haka shi ne, gwamnatin kasar Sin ta aiwatar da manufar gyaran fuska a gida da bude kofa ga ketare, kana kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa a cikin harkokin kasa da kasa, haka kuma ta taimaka wajen kyautata tsarin kasa da kasa, duk wadannan na kara habaka cudanyar tattalin arziki a fadin duniya."
Mozambick tana kudu maso gabashin nahiyar Afirka, tsayin yankin kasar dake gabar teku ya kai sama da kilomita 2600, saboda haka ta shiga shawarar ziri daya da hanya daya da kasar Sin ta gabatar. Chissano shi ma ya yaba da hadin gwiwar dake karkashin jagorancin shawarar matuka, ya ce, kasar Sin tana samar da taimako ga kasarsa wajen hakar ma'adinai, a sanadin haka, ba ma kawai al'ummun kasar Mozambick sun samu wadata ba, har ma an kyautata manyan kayayyakin more rayuwar jama'a a kasar; Misali an gina hanyar mota da layin dogo a kasar. A bayyane take cewa, tattalin arzikin kasar Mozambick ya samu ci gaba cikin sauri karkashin taimakon kasar Sin, ya ce, "Mozambick ta gabatar da bukatarta, kasar Sin ita ma ta gabatar da bukatar ta, ta haka sassan biyu sun kai ga gudanar da hadin gwiwa tsakaninsu, haka kuma za su samu moriya tare."
Chissano yana ganin cewa, shawarar ziri daya da hanya daya tana da babbar ma'ana, saboda ta cikin ta ana gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa bisa tushen hakuri da juna ba tare da rufa rufa ba, kana ana gudanar da hadin gwiwa tsakanin bangarori uku ko hudu. Ko shakka babu kasashen da suka shiga shawarar za su samu babbar moriya daga cikin ta, yana mai cewa, "Shawarar ziri daya da hanya daya ta samar da damammaki ga kasashen duniya, ta fuskar kara cudanya tsakaninsu, haka kuma ta ciyar da hadin gwiwa da zuba jari da cinikayya maras shinge gaba kamar yadda ake fata. Ana iya cewa, daukacin kasashen da suka shiga shawarar za su samu moriya daga cikin ta."(Jamila)