in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaro ya nuna damuwa game da yanayin tsaro a Afirka ta yamma
2018-01-12 10:50:10 cri

Kwamitin tsaron MDD ya nuna damuwa game da kalubalen tsaro da ake fuskanta a yankunan yammacin Afirka da na Sahel. Da yake bayyana matsayar kwamitin na tsaro, shugaban karba karba na kwamitin na wannan wata, kuma jakadan kasar Kazakhstan a MDDr Kairat Umarov, ya ce matsalar ta'addanci da yaduwar tsattsauran ra'ayi a wadannan yankuna abu ne mai tayar da hankali. Kuma hakan na da alaka da yaduwar muggan laifuka na kasa da kasa.

Mr. Umarov ya ce, daukacin mambobin kwamitin tsaron sun amince da bukatar daukar matakan shawo kan wadannan matsaloli, musamman a sassan tafkin Chadi da yankin Sahel.

Kaza lika a cewar jami'in, gamayyar kasa da kasa sun amince da ayyukan rundunar hadin gwiwar sojojin kasashen Burkina Faso, da Chadi, Mali, da Mauritania da Nijar wajen yaki da 'yan ta'adda da masu tsattsauran ra'ayi dake addabar yankin na Sahel.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China