in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Putin zai gana da Trump a Paris cikin watan Nuwamba
2018-10-24 10:14:21 cri

Mai taimakawa shugaban kasar Rasha Yury Ushakov ya bayyana a jiya cewa, shugaba Vladimir Putin zai gana da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump a birnin Paris na kasar Faransa a watan Nuwamba dake tafe.

Kamfanin dillancin labarai na kasar ta Rasha, ya ruwaito Ushakov na cewa, shugaba Putin ya gana da mai taimakawa shugaba Trump kan harkokin tsaron kasa John Bolton, wanda ke ziyara a kasar, inda suka tabbatar da cewa, shugabannin kasashen biyu wato Vladimir Putin da Donald Trump, za su gana da juna yayin da suke halartar bikin tunawa da cika shekaru 100 da kammala yakin duniya na farkon da za a shirya a birnin Paris a wata mai zuwa.

Ushakov ya bayyana cewa, ganawar da shugabannin biyu za su yi tsakaninsu irin ta yau da kullum ce, duk da cewa a halin da ake ciki yanzu, huldar dake tsakanin kasashen biyu ba ta gudana yadda ya kamata, amma ziyarar da Bolton ke yi a Rasha ta nuna cewa, gwamnatin Amurka tana son yin shawarwarin siyasa da gwamnatin Rasha, haka kuma bangaren Rasha shi ma yana wannan manufa.

Bolton ya sauka a birnin Moscow ne a ranar 21 ga wata, inda ya yi shawarwari da ministan harkokin wajen kasar da ministan tsaron kasar daya bayan daya, inda suka tattauna kan batutuwan da suka shafi huldar dake tsakanin kasashensu da yanayin da kasashen Syria da Afganistan ke ciki da yarjejeniyar kawar da makamai masu linzami masu cin gajere da matsakaicin zango da shugabannin kasashen biyu suka daddale a shekarar 1987 da kwance damara kan makaman nukiliya da sauransu.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China