in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in Najeriya: CIIE ya kara samar wa kasashe daban daban damar samun ci gaba
2018-11-08 20:00:25 cri
Babban sakataren ma'aikatar masana'antu, cinikayya da zuba jari ta kasar Najeriya Sunday Akpan ya bayyana a yau Alhamis a birnin Shanghai, cewa bikin baje kolin kasa da kasa na farko na kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin (CIIE) zai kara hadin kan kasashe daban daban, har su samu damar ci gaba mai kyau sakamakon bikin, ciki har da Najeriya.

Sunday Akpan shi ne ya jagoranci tawagar ma'aikatar masana'antu, cinikayya da zuba jari ta tarrayar kasar Najeriya wajen halartar bikin na CIIE, har ma ya shirya dandalin tattaunawa kan cinikayya da zuba jari na Najeriya na shekarar 2018 a safiyar yau Alhamis. Dandalin tattaunawar ya kasance daya daga cikin ayyukan bikin baje kolin na CIIE. An kuma shirya shi ne da nufin gabatar da wasu matakan kasar Najeriya game da harkokin zuba jari, ciki har da aikin gona, ma'adinai, kadarar gidaje, man fetur da iskar gas da kuma hada-hadar kudi da dai sauransu, tare kuma da inganta mu'amala a tsakanin kamfanonin Sin da Najeriya.

Jami'an ma'aikatar masana'antu, cinikayya da zuba jari ta kasar Najeriya, jami'an hukumomin da batun ya shafa, wakilan kamfanoni, jami'an diflomasiyyar kasar dake Sin, da kuma wakilan kamfanoni da jami'an majalisar kasuwanci na kasar Sin, wadanda yawansu ya wuce 100 ne suka halarci dandalin

A yayin da yake zantawa da wakilin gidan rediyon CRI, Sunday Akpan ya bayyana cewa, kasashen Sin da Najeriya na da makoma mai kyau wajen hadin kai, kasarsa na fatan cin gajiya daga bikin na CIIE da shawarar "Ziri daya da hanya daya".

Baya ga haka, ya kuma bayyana cewa, bisa yanayin da muke ciki na karfafa dunkulewar tattalin arzikin duniya bai daya, babu kasar da za ta iya neman ci gaba ita kadai, kasar Sin na kokari wajen gabatar da shawarar kasancewar bangarori da dama, da kara bude kofa ga kasashen ketare, wadannan muhimman matakai ne da ta dauka don biyan bukatun yanayin da ake ciki. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China