Madam Chibesakunda ta bayyana cewa, kamfanoni matsakaita da kanana na kasar Zambia da dama, sun halarci bikin CIIE, tare da kawo kayayyakinsu, kuma dukkanin kamfanonin sun yi farin ciki sosai da cimma yarjejeniyoyi da dama. Ta kuma yi imanin cewa, kamfanonin za su yi amfani da kudin shiga, a sakamakon yarjejeniyoyin, wajen inganta karfinsu na samar da kayayyaki da kyautata matsayin masana'antu. Wannan matakin zai sa kaimi ga raya masana'antu a Afirka, bisa tsarin dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar Sin da Afirka.
Har wa yau, kasar Sin ta kara bude kofa ga kamfanoni matsakaita da kanana na kasar Zambia, wanda hakan zai sa kaimi ga yin ciniki, da raya masana'antu a kasar Zambia. (Zainab)