Da yake karin haske yayin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Charles Onunaiju ya bayyana cewa, bikin na CIIE ya samar da wata babbar kasuwa mai bukatar hajoji, inda ya bayyana bikin na CIIE wanda shi ne irinsa na farko a matsayin, kasuwar duniya.
A cewarsa, idan kasashen dake wakiltar nahiyar Afirka suka yi kyakkyawan tasiri a yayin bikin baje kolin, hakan zai ba da babbar dama ga karin kasashen Afirka.
A yayin bikin baje kolin, Najeriya, kasa mafi karfin tattalin arziki a Afirka, tana baje kolin albarkatun ma'adinai da mai da iskar gas da fina-finai da wakoki da ma kayayyakin amfanin gona da Allah ya hore mata. (Ibrahim)