in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan cinikin Senegal: CIIE ya samar da dandalin samun ci gaba ga kamfanonin kashen duniya
2018-11-07 15:32:07 cri

An kaddamar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa kasar Sin daga ketare na kasa da kasa karo na farko wato CIIE a birnin Shanghai a ranar 5 ga wata. Yayin bikin, ministan kula da cinikayya da kafa kamfanoni na kasar Senegal wanda ke halartar bikin Alioune Sarr, ya zanta da wakilinmu, inda ya bayyana cewa, bikin CIIE, gaggarumin biki ne da ake gudanarwa, wanda ke samarwa kamfanonin kasashen duniya wani dandali na samun ci gaba.

A nasa bangare, Alioune Sarr ya bayyana cewa, manufar bude kofar da gwamnatin kasar Sin take aiwatarwa, za ta kara jawo hankalin 'yan kasuwa da su kara zuba jari a kasar, haka kuma za ta kara karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin bangarori biyu, ko bangarori da dama, kana za ta kara yawan ribar da kamfanonin za su samu, tare kuma da samar da karin damammakin aikin yi ga masu bukata. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China