in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Angola tana fatan Sin za ta zuba jari ga kasar a fannin yawon shakatawa ta hanyar bikin CIIE
2018-11-07 13:50:59 cri
Babban jami'in hukumar sa kaimi ga sha'anin yawon shakatawa ta ma'aikatar harkokin yawon shakatawa ta kasar Angola Simão Manuel Pedro, ya bayyana a wurin bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin wato CIIE a jiya cewa, kasarsa ta Angola tana fatan yin amfani da damar bikin CIIE don sa kaimi ga kasar Sin ta zuba jari ga kasar Angola a fannin yawon shakatawa da sauransu.

Mr Pedro ya bayyana cewa, babban makasudin kasar Angola na halartar bikin CIIE shi ne, taimakawa kasar wajen fadada kasuwar yawon shakatawa ga kasar Sin, da jan hankalin Sinawa zuwa kasar Angola don yawon shakatawa. Hakazalika kuma, kasar Angola ta gayyaci kamfanonin Sin masu zaman kansu da su zuba jari a fannonin aikin gona da masana'antu da yawon shakatawa da kamun kifi da sauransu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China