A cewar hukumar kwallon kafan kasar Kenya, wasu 'yan wasan kasar 4 dake zaune a kasashen waje suma zasu hadu da babbar tawagar 'yan wasan kasar a lokacin da zasu shiga sansanin horas da 'yan wasan a ranar Juma'a mai zuwa a Nairobi.
Kungiyar wasan tana shirye shiryen shiga zagayen farko na wasan share fagen kasashen Afrika 'yan kasa da shekaru 23, inda kasar Kenya zata fafata da Mauritius a wasan farko a ranar 14 ga watan Nuwamba, kafin daga bisani ta buga wasa na gaba kwanaki 4 bayan wasan data buga.
Da yake jawabi a ranar Lahadi, shugaban tawagar 'yan wasan kuma tsohon babban jami'in kungiyar wasan, Francis Kimanzi, ya amince da yin garambawul a tawagar 'yan wasan wanda aka gabatar mai dauke da kwararru 57.
"Hakika babban kalubale ne saboda muna da kwararrun 'yan wasa a kowane matsayi, sai dai daga bangaren tarin kwararrun 'yan wasan da nake dasu da kuma babban kociyan kungiyar wasan (Sebastien Migne), da mataimakinsa (Nicolas Borriquet-Cor), mun fito da 'yan wasa 18 wadanda zasu fara samun horo a makon gobe," inji shi.
Za'a buga wasan kwarshe na gasar cin kofin kasashen Afrika na 'yan kasa da shekaru 23 ne a watan Nuwambar shekarar 2019, a Masar, wanda zai kasance a matsayin share fagen shiga gasar wasannin Olympics na shekarar 2020.(Ahmad Fagam)