in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kalaman shugaba Xi yayin bude baje kolin CIIE sun nuna aniyar Sin ta fadada bude kofarta, in ji wani masani
2018-11-07 11:23:32 cri
Kalaman da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi, yayin bikin bude baje kolin kayayyakin da ake shigarwa kasar Sin irinsa na farko ko CIIE a takaice, sun nuna aniyar Sin, ta fadada bude kofarta ga kasashen waje.

Masanin al'amuran da suka jibanci kasar Sin, kuma shugaban cibiyar Kuhn, Mr. Robert Kuhn, shi ne ya bayyana hakan, cikin wani sakon email da ya aikewa kamfanin dallancin labarai na Xinhua a jiya Talata.

Mr. Kuhn ya ce jawabin shugaba Xi a baje kolin na birnin Shanghai, ya nuna jajircewar Sin a fannin bude kofa, ya kuma nuna faffadan tunanin shugaba Xi a fannoni da dama.

Ya ce Sin na da nufin ci gaba da bude kofofinta, da fadada sassanta na zuba jari, da samarwa duniya wata babbar kasuwa ta shigar da hajoji. A daya hannun kuma, ya kwatanta tattalin arzikin Sin da wani teku, ba wai 'yar korama ko gulbi, wanda wata guguwa za ta iya lalatawa cikin sauki ba.

Daga nan sai ya yi hasashen cewa, Sin za ta ci gaba da kokari na shawo kan duk wani kalubale da take fuskanta, za kuma ta cika alkawuranta na cimma nasara bisa tsarin moriyar juna, da aiwatar da manyan manufofin bunkasa cinikayya da zuba jari, da sakarwa kasuwanni mara, da karawa kasuwanni kuzari. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China