in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
DPRK za ta rufe cibiyar da take gwajin makaman nukiliyarta a watan Mayu
2018-04-29 16:39:15 cri
Fadar shugaban kasar Koriyar ta kudu ta sanar a yau cewa, shugaban Kim Jong Un na Koriya ta arewa ya sanar da cewa, kasarsa za ta rufe babbar cibiyar da ta ke gwajin makaman nukilyarta a watan Mayu.

Babban sakataren watsa labaran shugaba Moon Jae-in na Koriya ta Kudu, ya shaidawa taron manema labarai cewa, yayin ganawar da shugabannin biyu suka yi a ranar 27 ga watan Afrilu, shugaba Kim ya sanarwa takwaransa na Koriya ta kudu Moon Jae-in cewa, zai shirya yadda duniya za ta kalli yadda za a rufe cibiyar gwajin makaman nukiliyar kasar.

Shugaba Kim dai ya ce zai gayyaci kwararru da manema labarai daga kasashen Koriya ta kudu da Amurka zuwa Koriya ta arewa don su kalli yadda za a rufe cibiyar.

Bayanai na nuna cewa, Koriya ta arewa ta gudanar da dukkan gwaje-gwajenta na nukilya guda 6 a cibiyar Punggye-ri dake kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China