in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara aiki da babbar gadar Hong Kong-Zhuhai-Macao
2018-10-23 21:27:52 cri

A yau Talata ne, shugaban kasar Sin ya halarci bikin fara aiki da babbar gadar Hong Kong-Zhuhai-Macao, wanda aka shirya a birnin Zhuhai na kasar, inda kuma a hukumance ya sanar da fara aiki da gadar.

An dai shafe tsawon shakaru 15 wajen gina gadar, kuma gadar tana da tsawon kilomita 55, kana kuma ta hada birnin Zhuhai da kuma yankunan musamman na Macao da Hong Kong na kasar. Bayan fara aiki da gadar, lokacin zirga-zirgar motoci a tsakanin Hong Kong da Zhuhai da kuma Macao, zai ragu daga awa 3 zuwa minti 45. Bisa bayanin babban mai tsara fasalin gadar Meng Fanchao, gadar za ta kawo babban sauyi ga zaman rayuwa, da tattalin arziki, da kuma yanayin zirga-zirga a shiyyar.

Kirkire-kirkire ne suke samar da rayuwa mai dadi. A yayin da ake gina gadar, an sha yin amfani da sabbin kayayyaki, da fasahohi da kuma na'urori na zamani. A cewar Su Quanke, babban injiniyan kula da gadar, "Gadar Hongkong-Zhuhai-Macao ta cancanci sunanta ta gadar fasahohin zamani, kuma gadar kirkire-kirkire."

Ga misalin, domin tinkarar manyan kalubaloli guda hudu da ake fuskanta a fannonin ginawa da gudanarwa, da fasahohin ginawa, da kiyaye muhalli da kuma tabbatar da tsaro a teku, an bi manufar masana'antu wajen gina gadar Hong Kong-Zhuhai–Macao, wadda ke iya tinkarar mahaukaciyar guguwa mai digiri 16, da girgizar kasa mai digiri 7, za kuma ta iya aiki har tsawon shekaru 120. Wannan ne kuma karo na farko da ake bin hanyar ginawa ta masana'antu a tarihin gina gadar dake keta teku a duniya. Ban da wannan kuma, wasu fasahohin da ake amfani da su wajen gina gadar sun karya matsayin bajinta na duniya.

Abin da ya tantance a ambata shi ne, a yayin da ake gina wannan gadar, yawan irin dabar nan ta ruwa ta musamman ta kasar Sin wato "chinese white dolphin" ya karu daga 1200 a shekarar 2010 zuwa 2000 da wani abu a yanzu, hakan ya tabbatar da zaman tare yadda ya kamata, a tsakanin dan Adam da halittu. Sabo da haka, ake kiran gadar Hong Kong-Zhuhai-Macao da "Tsaunin Everest" a fannin gada, kuma "Alama ta kasar Sin ta matsayin babbar kasa a fannin gada zuwa kasa mai karfi a fannin gada". Jaridar The guardian ta kasar Burtaniya ta mai da ita daya daga cikin "Sabbin manyan abubuwa masu ban mamaki a duniya".

Babbar gadar Hong Kong-Zhuhai-Macao ta zama wani sabon abun misali, ga sana'ar yin kirkire-kirkire ta kasar Sin. Tarihi ya nuna cewa, ra'ayin yin kirkire-kirkire, na daya daga cikin kyawawan halayen al'ummar kasar Sin, wanda ya bada babban karfi ga ci gaban kasar.

Tun da aka fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje shekaru arba'in da suka wuce, musamman ma shekaru biyar da suka gabata, gwamnatin kasar Sin tana kokarin neman samun ci gaba ta hanyar yin kirkire-kirkire, kuma al'ummar kasar na himmatuwa wajen neman samun kyautatuwar zaman rayuwa ta hanyar yin kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha. A shekara ta 2017, yawan gudummawar da ci gaban kimiyya da fasaha ya bayar ga habakar tattalin arzikin kasar Sin, ya dauki kashi 57.5 bisa dari, wanda ya tasam ma burin kashi 60 bisa dari zuwa nan da shekara ta 2020.

Kana, adadin yawan sabbin abubuwan da aka kirkiro su a kasar Sin ya zarce miliyan 1.3, wanda ya kai matsayin koli a cikin jerin shekaru bakwai. A nasa bangaren, wanda ya kaddamar da dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya, kana shugaban zartaswar dandalin, wanda kuma ya ganewa idanunsa yadda kasar Sin ke aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, Mr. Klaus Schwab ya bayyana cewa, a halin yanzu kasar Sin na kokarin raya sana'o'in yin kirkire-kirkire don neman samun bunkasuwa.

Mun yi imanin cewa, kaddamar da babbar gadar Hong Kong-Zhuhai-Macao, zai kara taimakawa wajen raya sana'o'in kirkire-kirkire a babban yankin Guangdong, da Hong Kong, da kuma Macau, ta yadda za'a kara samun ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, gami da kyautatuwar zaman rayuwar al'ummar kasar. (Ma'aikatan sashen Hausa: Lubabatu Lei, Bilkisu Xin, Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China