in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta harba tagwayen taurarin dan Adam samfurin BeiDou-3
2018-10-15 19:35:02 cri

Da misalin karfe 12 da mintuna 23 na tsakar ranar yau Litinin ne kasar Sin ta harba tagwayen taurarin dan Adam samfurin BeiDou-3. Taurarin masu aikin ba da hidima a ayyukan sufuri, an harba su ne ta hanyar amfani da rokar Long March-3B, daga tashar harba kunbuna ta Xichang, dake lardin Sichuan na nan kasar Sin.

Taurarin dan Adam din sun shiga falakin su bayan shafe sa'o'i 3 suna keta hazo, za kuma su yi aiki tare da rukuni na 14 na taurarin dan Adam samfurin BeiDou-3, wanda tuni ke can a sararin samaniya.

Wadannan taurarin dan Adam dai su ne na 39 da 40, a rukunin taurarin BeiDou masu aikin bada hidima a fannin sufuri, kana su ne na 15 da 16, a jerin rukunin taurarin BeiDou-3. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China