in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta harba tagwayen taurarin dan-Adam na Beidou-3
2018-09-20 11:21:03 cri
Jiya Laraba ne kasar Sin ta yi nasarar harba tagwayen taurarin dan-Adam na zirga-zirga na Beidou mai lamba 3 zuwa sararin samaniya, ta hanyar amfani da roka.

An harba rokar Long march samfurin 3B dake dauke da taurarin dan-Adam din ne daga cibiyar harba taurarin dan-Adam ta Xichang da karfe 10.07 na daren ranar Laraba. Kuma wannan shi ne aiki na 285 da jerin rokokin na Long March suka gudanar.

Tagwayen taurarin dan-Adam din za su rika samar da bayanan gargadi game da hadari da ayyukan zirga-zirga ga masu bukatu a duniya. Ana kuma fatan nan da karshen wannan shekara, za a samar da wani tsarin da taurarin dan-Adam na Beidou mai 3 guda 18 za su rika kewaye duniya, tsarin da ake fatan zai samar da hidima ga kasashen da ke cikin shawarar ziri daya da hanya daya.

A shekatar 2000 ne kasar Sin ta fara amfani da tsarin na Beidou, yayin da yankin Asiya da Fasifik ya fara cin gajiyar tsarin a 2012.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China