in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwararru sun koka kan yadda manoma ke hasarar amfanin gona a nahiyar Afirka
2017-09-28 09:27:52 cri

Darektar gidauniyar kasa da kasa mai kula da harkar samar da abinci wato Rockefeller foundation Betty Kibaara, ta bayyana cewa, nahiyar Afirka tana hasarar kimanin kaso 50 cikin 100 na kayan marmari da ganyaye da kuma kaso 40 cikin 100 na doya, baya ga kaso 20 cikin 100 na alkama da ake nomawa ko wace shekara.

Madam Betty ta bayyana hakan ne lokacin da take jawabi a taron samar da abinci da bikin baje kolin amfanin gona na Afirka na shekarar 2017 da ya gudana a birnin Nairobin kasar Kenya. Ta ce, matsalolin da manoman nahiyar ke fuskanta sun hada da rashin kasuwannin da za su kai amfanin da suka noma, da dogaro kan ruwan sama, lamarin da ya sa galibin amfanin gonan isa kasuwanni a lokaci guda, da karancin abubuwan adana amfani gona na zamani.

A don haka ta yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa, da su bullo da nagartattun matakai don magance matsalar hasarar amfanin gona da nahiyar Afirka ke tabkawa, wanda aka yi kiyasin cewa, ta kai dala biliyan 4 a ko wace shekara.

Ta ce, a nata bangare, gidauniyar ta bullo da irin shuka na zamani wanda zai rage irin hasarar da nahiyar take tabkawa da kaso 50 cikin 100 nan da shekaru bakwai masu zuwa. Yanzu haka, an fara aiwatar da wannan shiri a kasashen nahiyar uku da suka hada Najeriya, Kenya da kuma Tanzaniya.

Gidauniyar ta Rockefeller ta kuma bayyana cewa, idan har nahiyar Afirka ta kartata ga amfani da fasahohi na zamani da samun horo, hakika za ta iya rage hasarar amfanin gonan da ta ke yi, (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China