in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron dandalin tattaunawa karo na 2 kan hanyar siliki ta teku ta karnin 21
2018-09-20 09:31:50 cri

A jiya Laraba, aka bude taron dandalin tattaunawa karo na 2 kan hanyar siliki ta teku na karnin 21 a birnin Zhuhai na kasar Sin, wanda babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG da gwamnatin lardin Guangdong suka karbi bakuncin gudanar da shi. Taken taron tattaunawar shi ne "sabuwar hanyar siliki ta teku a sabon zamanin da ake ciki", manufar taron ita ce gadan tunanin tarihi da shigar da sabon tunani a sabon zamanin da ake ciki.

Shugaban babban rukunin CMG Shen Haixiong ya bayyana a gun bikin bude taron cewa, shekarar bana shekara ce ta cika shekaru 40 da aiwatar da manufar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga kasashen waje a kasar Sin, kana shekara ce ta cika shekaru 5 da shugaba Xi Jinping ya gabatar da shawarar "ziri daya da hanya daya". Taron tattaunawar na wannan karo zai shaida sabbin nasarorin da aka samu wajen aiwatar da shawarar raya hanyar siliki ta teku cikin kanin 21, da kuma aikin yin mu'amala da juna a fannin al'adu. Babban rukunin CMG zai ci gaba da watsa ra'ayoyin Sin, da kiyaye tsarin yin ciniki a tsakanin bangarori daban daban da watsa labaru game da tunanin al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama.

Lardin Guangdong wuri ne da aka fara aiwatar manufar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga kasashen waje a kasar Sin, kana muhimmin yanki ne na raya hanyar siliki ta teku. Gwamnan lardin Guangdong Ma Xingrui ya yi jawabi cewa, Lardin ya hada gwiwar kasashen a fannonin tsara manufofi da gina ayyukan more rayuwa da saukaka harkokin ciniki da zuba jari da kuma cudanyar jama'arsu. Ya yi imani da cewa, bisa ga taron dandalin, bangarori daban daban za su kara yin mu'amala da juna, ta yadda za su cimma daidaito kan fadada hadin gwiwarsu.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China