Rahoton da bankin ya fitar jiya a Nairobi, ya ce ma'aunin CPIA na kasashen kudu da hamadar sahara, wanda bankin ke amfani da shi wajen tantance taimakon da zai ba kasashe mafi talauci a duniya da aka kaddamar tun a shekarar 1980, ya ba da sakamako mai kyau game da ingancin dabarun kasashen Afrika, wanda ya bunkasa tattalin arzikin nahiyar.
Babbar mai nazarin tattalin arziki ta Bankin a nahiyar Afrika, Punam Chuhan-Pole, ta ce a shekarar 20017, kasashen Afrika sun samu kyakkyawan yanayi da ya samar musu da damar aiwatar da gyare-gyare.
Ta ce bisa binciken da suka gudanar, kusan kaso 30 na karin wasu kasashe, sun karfafa ingancin dabaru da tsarukansu idan aka kwatanta da shekarar 2016, abun da ta bayyana a matsayin mai karfafa gwiwa.
Rahoton CPIA na 2017, ya yi nazarin ayyukan dabaru da tsarukan tattalin arziki a kasashen Afrika 38, da suka cancanci samun taimakon raya kasa na bankin, wanda ake ba kasashe mafi koma baya ta fuskar tattalin arziki. (Fa'iza Mustapha)