in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha ta shiga sabon zamani
2018-09-12 15:04:59 cri

Jiya Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin a Vladivostok, inda baki daya shugabannin biyu suke tabbatar da cewa, a cikin shekarar nan, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu na samun ci gaba cikin yakini, ta kuma shiga sabon zamani na samun saurin bunkasuwa bisa babban matsayi. Ban da wannan kuma, sun amince da cewa, duk da canje-canjen da duniya ke fuskanta, Sin da Rasha za su ci gaba da raya dangantakarsu yadda ya kamata, da ma kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.

Aiki na farko da Xi Jinping ya yi bayan ya isa Vladivostok, shi ne halartar shawarwari a tsakaninsa da shugaba Putin, wanda hakan ya jawo hankulan mutane sosai. Wannan ne karo na uku da ya gana da Putin, shi ne kuma karo na 26 da aka yi shawarwari a tsakaninsu tun daga shekarar 2013. A cewar Xi Jinping,

"A cikin kusan watanni hudu da suka wuce, na riga na yi shawarwari tare da shugaba Putin har sau uku, irin wannan cudanya mai armashi ta nuna babban matsayi, da halin musamman na dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha, ta kuma nuna matsayin fifiko na dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, wanda suke aiwatarwa a fannin ayyukan diplomasiyyarsu. A cikin shekarar nan kuma, za mu yi ganawa game da wasu muhimman ayyukan na bangarori da dama, don ci gaba da yin cudanyar sada zumunta sosai."

Xi Jinping ya nuna cewa, kokarin da bangarorin biyu suke yi, da fifikon da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ke nunawa a fannin siyasa, na juyawa zuwa hakikanan nasarorin hadin kai.

"Ni da shugaba Putin, baki daya muna ganin cewa, dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha na samun ci gaba cikin yakini a bana, har ma ta shiga wani sabon zamani na samun saurin bunkasuwa bisa babban matsayi. Bangarorin biyu na tsayawa kan nuna goyon baya ga juna, wajen bin hanyar raya kasa da ta dace, da kiyaye tsaronsu, da 'yancinsu na ci gaba, wanda ya zama abin koyi ga duniya kan yadda za a samu damar raya dangantaka a tsakanin manyan kasashe, da kasashe makwabta."

Xi ya kuma jaddada cewa, Sin da Rasha za su karfafa raya shawarar "ziri daya da hanya daya", da kuma laimar kawancen tattalin arzikin Turai da Asiya, kana da kyautata hadin kansu a fannonin makamashi, ayyukan gona, kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, da ma sha'anin kudi da sauran muhimman fannoni.

Bayan haka kuma, Xi Jinping ya nuna cewa, nuna goyon baya ga juna kan manyan ayyukan da kasashen biyu suke yi, kyakkyawar gargajiya ce ta kasashen Sin da Rasha. Shugaba Putin shi kan sa ya ba da shawara, ta shirya dandalin tattaunawar batun tattalin arziki na yankin gabashin duniya. Ya zuwa yanzu dandalin ya riga ya kasance wani muhimmin dandamali na tattara hazaka, da yin shawarwari tare kan hadin kan shiyyar. Xi Jinping ya yi imanin cewa, dandalin na wannan karo zai samar da sabuwar dama wajen zurfafa hadin kai a kananan wurare, ciki har da hadin kai a yankin gabas mai nisa.

Xi Jinping ya kuma jaddada cewa, a matsayinsu na masu kujerun dindindin a kwamitin sulhu na MDD, kuma sabbin kasuwanni masu tasowa, kasashen Sin da Rasha ma na daukar babban nauyi na kiyaye zaman lafiya da zaman karko, da inganta bunkasuwa, da samun wadata a duniya.

A nasa bangaren, shugaba Putin ya bayyana cewa, ya yi godiya da maraba sosai kan halartar shugaba Xi Jinping dandalin tattauna batun tattalin arziki na yankin gabashin duniya bisa gayyatar da ya yi masa. Ya ce, yana cudanya sosai tare da shugaba Xi Jinping, hakan ya nuna muhimmancin dangantakar dake tsakanin Rasha da Sin.

"Mun yi shawarwari, inda muka tattauna hakikanan batutuwan bangarorin biyu da na kasa da kasa, kana mun tsara shirin kara ci gaban dangantakar abokantakar hadin kai bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni. Na yi imanin cewa, jerin cudanya da za mu yi a yayin dandalin, za su yi amfani wajen bunkasuwar kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu."

Baya ga haka, Putin ya bayyana cewa, bangarorin biyu za su ci gaba da inganta kawancen tattalin arzikin Turai da Asiya da ma hadin kan shawarar "Ziri daya da hanya daya", da kuma habaka hadin kai a fannonin zuba jari, makamashi, zirga-zirgar sararin samaniya, sha'anin kudi, da cinikin Intanat, kana da kara cudanyar mutane, da ma kara azama wajen hadin gwiwar kananan wuraren kasashen biyu. Ya kuma furta cewa, Rasha da Sin na da ra'ayi daya, game da halin da kasashen duniya ke ciki yanzu. Kuma ya kamata su kara hadin kai a cikin lamuran duniya, da yaki da ra'ayin kashin kai, a kokarin kiyaye dokokin kasa da kasa cikin adalci da samun wadata gaba daya. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China